…Sun harbe ’yan fashi biyu a danja

A wani labarin kuma, rundunar ’yan sandan ta yi nasarar kama wasu ’yan fashi yayin da wasu mutun biyu daga cikinsu suka sheka lahira sanadiyar musayar wuta da suka yi a garin Tandama da ke cikin karamar Hukumar danja, Jihar Katsina. Wannan al’amari ya faru ne bayan da wasu gungun ’yan fashi suka je gidajen […]

…Sun harbe ’yan fashi biyu a danja

A wani labarin kuma, rundunar ’yan sandan ta yi nasarar kama wasu ’yan fashi yayin da wasu mutun biyu daga cikinsu suka sheka lahira sanadiyar musayar wuta da suka yi a garin Tandama da ke cikin karamar Hukumar danja, Jihar Katsina.

Wannan al’amari ya faru ne bayan da wasu gungun ’yan fashi suka je gidajen Alhaji Abdullahi da kuma Alhaji Safiyanu dukkansu mazauna garin na Tandama, inda suka yi fashi amma ’yan sanda na yankin da aka sanar da su abin da ke faruwa, suka nufi garin, a inda suka hade da ’yan fashin a lokacin da suke kokarin fitowa daga garin; inda suka yi musayar harbe-harbe har biyu daga cikin ’yan fashin suka mutu nan take. ’Yan sandan sun ce suna ci gaba da bincike, domin mika wadanda ake tuhuma zuwa kotu.