Sun kai karar asibiti bisa haifar namiji maimakon mace
Ma’auratan yanzu haka suna tuhumar asibitin da laifin rashin da’a da kuma saba kwantaragi da sauransu.
Wadansu ma’aurata da ke birnin Buffalo a Jihar New York ta Amurka sun kai karar wani asibitin karbar haihuwa da suka yi alkawarin tantance jinsin dan tayi kafin a dasa shi a cikin mahaifar matar, inda ma’auratan suka samu da namiji ba mace ba.
Ma’auratan masu suna Heather da Robin WilhelmRoutenberg sun yanke shawarar haihuwar ce kawai, idan za a iya ba su tabbacin cewa mace ce, saboda raunin tunani da Heather ta fuskanta a baya a rayuwarta.
- ‘Yan siyasa 9 za su janye wa Ahmed Lawan takarar Shugaban Kasa —Orji Kalu
- Dakarun MNJTF sun kashe shugabannin ISWAP 3 a gabar Tafkin Chadi
Don haka, ma’auratan suka je asibitin haihuwa na CNY da ke Latham, a New York, wanda aka ba su tabbacin cewa za a iya tantance jinsin dan tayin da aka yi ta amfani da kwan haihuwa daga jikin Robbie da maniyyin da ake rabawa.
Duk da haka, mako 15 da samun juna biyu na Heather, ma’auratan sun yi mamakin jin cewa da namiji za su samu, duk da ’ya mace suke nema.
Ma’auratan yanzu haka suna tuhumar asibitin da laifin rashin da’a da kuma saba kwantaragi da sauransu.
Heather WilhelmRoutenberg ta tattauna da jaridar New York Post, inda ta nuna kaduwa kan gano da namiji ne a cikin mahaifarta ba mace da suke nema ba.
Da alama ta gamsu cewa, tana iya haifar yarinya kamar yadda Asibitin CNY Clinic ya yi alkawari, har sai da likitan haihuwa ‘OB-GYN’ ya gaya mata sakamakon gwajin da ya nuna samun namiji.
“Lokacin da na fita waje, na ji sauyi a jikina. Na dauka cewa, tayin wani ne, ba kuskuren cikin namu ba ne,” inji Heather.
Ta ce, “Hakan ya tsoratar da ni. Ban san yadda zan bayyana wannan ba – na ji kamar akwai bakon abu da ke zaune a cikina.”
Heather ta tuna cewa, lokacin da ta fara jin labarin, ta yi tunanin tana dauke da jaririn wani ne, sakamakon kuskuren da asibitin ya yi na dasa mata wani tayi a jikinta.
Ba wannan kadai ba, wannan jaririn namiji ne abin da ya fara tsorata ta tun farko ke nan. Amma kasancewar dan tayin na wani ne, domin Heather ta fara gaya wa kanta cewa, za su iya cinikin jarirai da duk wanda dan ya kasance nasa ne, sannan za su samu jaririyar da Asibitin CNY ya yi alkawari.
Amma wannan mafarki bai tabbata ba lokacin da asibitin haihuwa ya tabbatar da cewa tayin nasu ne.
“Bayan mako bakwai mun samu sakon imel cewa, wannan tayin namu ne. Lallai jaririn namiji ne kuma hakika yana da alaka da Robbie. Babu wata jaririya da ake tsammani,” Heather ta bayyana.
Kodayake an ambaci zubar da ciki a matsayin wani zabi, kasancewar sun riga sun rasa ciki daya.
Sa’an nan kuma akwai abokan arziki da iyalai da suka yi musu murna farin sosai, amma Heather ba ta ji wani farin ciki bisa jaririn da ke girma a cikinta ba.
Al’amura sun kara dagulewa lokacin da aka haifi jaririn, a watan Disamban 2020. Heather ta yi mafarkin rike ‘yarta a kirjinta, amma bayan ta ga abin da ta haifa a nan ta kasa bari ya taba ta.
Tana sa kaya don kada ya taba kirjinta. Nan ta fara shiga damuwa, a lokaci guda ta yi tunanin ta haukace ne. Da yanzu jaririn yana da shekara daya da rabi, kuma abubuwa sun yi musu kyau sosai.
Robin da Heather suna ganin matsalar ta asibitin ce, domin kuwa da sun samu abin da suke so da ba haka ba. Don haka, suke ganin matakin da suka dauka ya dace a kan Asibitin CNY.