Sun karya matashi a Zariya kan fallasa satar kayan gwamnati

Wani matashi mai suna Habibu Yahaya ya gamu da fushin barayi dalilin tona asirinsu da ya yi. Matashin mai suna Habibu Yahaya dan shekara 22 yaron mota ne a Zariya da ke Jihar Kaduna.Matashin wanda ya kwashe kusan wata uku yana jinya a daki a gidansu da ke Tsohuwar Kasuwar danmagaji yana jinyar kafarsa da […]

Sun karya matashi a Zariya kan fallasa satar kayan gwamnati
Sun karya matashi a Zariya kan fallasa satar kayan gwamnati

Wani matashi mai suna Habibu Yahaya ya gamu da fushin barayi dalilin tona asirinsu da ya yi. Matashin mai suna Habibu Yahaya dan shekara 22 yaron mota ne a Zariya da ke Jihar Kaduna.
Matashin wanda ya kwashe kusan wata uku yana jinya a daki a gidansu da ke Tsohuwar Kasuwar danmagaji yana jinyar kafarsa da ta tasam ma rubewa a sanadiyyar karya shi da barayin suka yi, ya shaida wa Aminiya cewa, wani lokaci da daddare sun dawo daga tafiya da misalin karfe 1:00 na dare yana wanki a kofar daki, abokan sana’arsa suna mota suna barci saboda za su yi sammakon zuwa sauke kayan da suka dauko sai wadansu yaran unguwarsu kusan 12 suka zo dauke da kofofi a kansu suka ce ya ajiye musu shi kuma yace a’a domin gobe za su wuce kuma daga ina suke sai suka ce sun dawo tafiya ce dare ya yi musu don haka suke so su ajiye sai da safe su dauka.
Matashi Habibu ya ce ashe sun sato kofofin ne a makarantar je ka ka dawo wato (Day Secondary School) da ke kofar Kibo, Zariya wadda ake yi mata gyara. Ya ce ashe maigadin makarantar na biye da su kuma ya ga lokacin da muke magana shi kuma yana gudun kada ya fada musu su halaka shi don haka yake biye da su a hankali ya ga inda za su kai. “Da gari ya waye muna shirin tafiya ke nan sai ga maigadi da wasu mutane suna tambayata sai na ce musu ba su aje a nan ba sun wuce da abinsu amma na san su. Muna cikin haka sai ga daya daga cikin yaran zai wuce mai suna Bello Alagun wanda dan Mai unguwar kofar Jatau ne sai na ce masa yawa ga daya daga cikinsu nan sai aka kama shi aka yi masa tambayoyi ya fadi yadda abubuwan suke sannan suka dawo musu da kofofinsu. Sai iyayen yaran ciki har da Mai unguwa da aka kama dansa suka roki arziki cewa a yi hakuri tunda Allah Ya sa an ga kayan kuma an dawo da su a yafe kada a kai maganar gaban’yan sanda tunda wannan kaya na gwamnati ne idan aka kai wajen ’yan sanda yaran za su wahala. Aka bar maganar a nan masu kaya suka ba ni Naira dubu na ce a’a ba na so,” inji shi.
Ya ce, “Bayan mun yi tafiya mun dawo ashe yaran nan na kufule da ni suna jin haushin na tona musu asiri. Misalin karfe 4:00 na yamma muna tafiya za mu je gida tare da abokina suka tare mu suka ce sai sun halaka ni domin wai na tona musu asiri. Su ka yi ta barazana da wukake da sauransu, bayan su kyale mu mun wuce sai na je na sanar da mahaifiyata, ta ce to in je in sanar da ’yan sanda. Bayan na je na sanar da su muka zo nemansu ba su, don haka aka ce in an gan su za mu koma gaban ’yan sanda domin a shiga tsakanina da su, to wannan daren su 12 suka zo dakina da daddare misalin karfe 2:00 na dare suka fara jijjiga kofata har sai da suka balle suka dauko ni a wuya ina ihu. To dama a kusa da mu a bayan wannan makarantar da suka sato kofofin akwai rafi suka nufi nan da ni. Ni kuma ina ta ihu kafin mutane su zo sun dauki bulo sun faskara min a kafa sun dauko wukake za su yanka ni domin dayansu ya ce a yi min yankan rago. Sai ga jama’a sai suka wurga ni cikin rafi suka gudu, shi ne mutanen da suka zo suka dauko ni suka kai ni daki, sanna suka je suka sanar da mahaifiyata.”
Ya ce babansa ya rasu amma mahaifiyarsa ta sanar da ’yan sanda a zo aka tafi da su a lokacin an kama yara uku Bello Alagun da Magaji da Sunusi, sauran kuma sun tsere.  “To tunda an yi min dauri a kafa ina daki mahaifiyata ke bin kadin maganar. Daga nan aka tura mu kotu kuma har yanzu da yake an sake su sauran da suka gudu kuma sun dawo suna aiko da sakon cewa sai sun halaka ni kuma ga kafar ma yanzu a rube take domin wari take yi masu gyaran dori sun kasa saboda akwai rauni kuma yanzu haka ba ni da kudin zuwa asibiti mahaifiyata ce take dawainiya da ni,” inji shi.
Mahaifiyarsa mai suna Rakiya Isa ta shaida wa wakilinmu cewa bayan ’yan sanda sun kama mutane uku sa isuka taru su kotun gargajiya da ke Madaci, inda nan aka yi musu shari’a alkali ya kawo Naira dubu 22 ya ce ta je ta yi jinyar danta. Ta ce kudin sun kare kuma yaran suna yawo har suna aiko da muguwar magana cewa kadan ke nan ya gani sun sha alwashin cewa sai sun halaka shi kuma yanzu haka kafarsa ta rube kuma babu kudin zuwa asibiti. Ta ce “Wadancan da suka ga kayansu wanda a sanadiyyarsu aka yi wa dana haka ba su zo ko da gaida shi ba. Don haka nake bukatar don Allah hukuma ta sa baki domin dana ya samu lafiya,” inji ta.
A ofishin ’yan sanda na danmagaji, Babban Jami’insu (DPO) Kassim Abdul ya ce lallai ya kama mutum uku daga cikin yaran sauran kuma sun gudu kuma an gabatar da su gaban kotu inda suke farautar sauran amma har yanzu ba su samu damar kama su ba.
A Kotun Gargajiya (Customary Court) da ke Madaci, Alkalin Kotun S.B Wazi ya ce an yi shari’ar yara uku bayan ya kama su da laifi inda ya yi musu tara, biyu daga cikinsu sun biya tarar daya ya kasa biya ya tafi zai yi shekara uku a gidan yari kuma ya ba mahaifiyar yaron mai suna Rakiya kudi domin ta yi jinyar danta.
Sai dai Alkalin bai bayyanna ko nawa ya karba daga hannun yaran ba kuma bai fadi yawan kudin da ya ba mahaifiyar Bello domin ta yi jinyar danta ba.