Sun kashe shi saboda ganin shi da naman saniya a Indiya

Sun kashe mutumin da aka kama da naman saniya a Indiya

Sun kashe shi saboda ganin shi da naman saniya a Indiya

‘Yan sandan Indiya

’Yan sanda a Indiya sun kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a kisan wani Musulmi da suka zarga da mallakar naman saniya a jihar Bihar da ke Gabashin kasar.

Mutumin, Naseem Qureshi, mai kimanin shekara 56 ya rasu a farkon makon nan bayan wasu gungun mutane sun kai masa hari saboda ana zarginsa da mallakar naman saniya.

Wasu hukumomin kasar dai sun haramta ci, sayarwa ko ta’ammali da naman saniya saboda tsarkinsa a wasu sassan kasar, kasancewar akwai dimbin masu bauta mata a cikinta.

Wata sanarwar ’yan sanda a kotu ta nuna cewa sama da mutum 20 ne suka yi wa Naseem kawanya tare da yi masa dukan tsiya.

Daga bisani dai ’yan sanda sun shiga tsakanin, amma ya mutu a kan hanyar kai shi asibiti, in ji ’yan sandan.

Ramchandra Tiwari, Shugaban ofishin ’yan sanda da ke Jihar Rasulpur a Jihar ta Bihar, inda a can ne aka aikata kisan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Asabar cewa tuni aka kama mutum uku kan laifin.

Shanu dai na da tsarki a addinin Hindu na Indiya, kuma an jima ana kai wa wadanda ake zargin da kashe su saboda nama ko amfani da fatunsu, wadanda galibinsu Musulmai ne.

Mabiya addinin na Hindu dai sun jima suna fafutukar ganin an haramta ci ko yanka saniya a ilahirin fadin kasar ta Indiya.

Sai dai tun bayan hawan Fira Minista Narendra Modi kan karagar mulkin kasar a 2014, masu wannan fafutukar suka fara yunkurin ganin sun tilasta bin dokar da kansu.

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya