Sun koka kan lalacewar hanyar Bayamari zuwa Nguru
Al’ummar Jihar Yobe musamman masu bin hanyar Bayamari zuwa Nguru sun koka kan yadda hanyar ta lalace inda hakan ke jawo yawan hadari da tsaikon zirga-zirgar ababen hawa da haka ke shafar yanayin tattalin arzikin yankin. Hanyar wacce ta shafe sama da shekara 40 da gina ta kuma ta ratsa kananan hukumomi takwas na jihar, […]
Al’ummar Jihar Yobe musamman masu bin hanyar Bayamari zuwa Nguru sun koka kan yadda hanyar ta lalace inda hakan ke jawo yawan hadari da tsaikon zirga-zirgar ababen hawa da haka ke shafar yanayin tattalin arzikin yankin.
Hanyar wacce ta shafe sama da shekara 40 da gina ta kuma ta ratsa kananan hukumomi takwas na jihar, babu wani dauki da Gwamnatin Tarayya ta kai wa hanyar duk da muhimmancin da take da shi ga harkokin tattalin arzikin yankin da kasa baki daya.
Wani mai mai suna Baba Sa’idu Maijarida mazaunin garin Gashuwa ya shaida wa Aminiya cewa, “Duk mai bin hanyar tamu da ta taso daga kan iyakarmu da Jihar Jigawa zuwa Bayamari dole ya ji tausayin jama’armu, kuma duk inda ka taso a cikin kasar nan babu inda ranka zai baci kamar wannan tsakani sai ka ce ba a Najeriya muke ba.”
Ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta yi wa yankin nasu adalci ba, saboda ta maida su baya ga dangi ta fuskar ayyukan raya kasa musamman hanyoyin mota.
Shugaba Bulakolo Direba Koromari ya bayyana cewa, “Hanyar tana daga cikin hanyoyi mafiya muni a kasar nan kuma tana ci mana tuwo a kwarya domin duk kokarinka ko sabuwar mota ka saya zai yi wahala ta shekara lafiya ba ta lalace ba, saboda tsananin munin hanyar.”
Da Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Ayyuka na Jihar Yobe Injiniya Siraja Wakil kan hanyar, ya ce, “Wannan hanya ce ta Gwamnatin Tarayya kuma da dadewa ta bayar da ita gyara daga Nguru zuwa Gashuwa ga kamfanin GYARAWA, sannan ta bai wa wani kamfanin mutanen Chaina daga Gashuwa zuwa Bayamari, amma har yanzu kamfanonin ba su kammala aikin ba, kuma Gwamnatin Tarayya ba ta soke kwangilar ba. Saboda haka babu yadda za a yi gwamnatin jiha ta hau kan aikin hanyar ba tare da an tabbatar da cewa an soke kwangilar da ta ba su ba.”
Injiniya Siraja Wakil ya ce, “amma cikin ’yan kwanakin nan mun ba Mai girma Gwamna Ibrahim Gaidam shawara kan ya tuntubi Ministan Ayyuka kan a matsa wa kamfanonin su zo su ci gaba da aikin ko a soke kwangilar a ba wasu.”