Sun koka kan yunkurin Gwamnatin Legas na rushe Kasuwar Gatan-Kowa

’Yan kasuwar Gatan-Kowa da ke yankin Abulegba a Jihar Legas sun koka kan yunkurin da gwamnatin jihar ke yi na tashin kasuwar da gidajensu da ke Unguwar Gatan-Kowa a Legas, lamarin da suka ce zai sanya su cikin kunci. Wani matashi mai suna Tasi’u Idris da ke kasuwanci a Kasuwar Gatan-Kowa ya shaida wa Aminiya […]

Sun koka kan yunkurin Gwamnatin Legas na rushe Kasuwar Gatan-Kowa

’Yan kasuwar Gatan-Kowa da ke yankin Abulegba a Jihar Legas sun koka kan yunkurin da gwamnatin jihar ke yi na tashin kasuwar da gidajensu da ke Unguwar Gatan-Kowa a Legas, lamarin da suka ce zai sanya su cikin kunci.

Wani matashi mai suna Tasi’u Idris da ke kasuwanci a Kasuwar Gatan-Kowa ya shaida wa Aminiya cewa, ’yan kasuwar sun share sama da shekara 40 suna harkokinsu a kasuwar.

“Kasuwar Gatan-Kowa kasuwa ce mai albarka da dimbin mutane ke cin abinci a cikinta ta kasu kashi uku, akwai masu sayar da kayan sawa na gwanjo wadanda su ne suka fi yawa, sai masu sana’r karafa na ’yan gwangwan  da masu sayar da kayan manyan motoci, baya ga mu da ke saye da sayarwa akwai dubban masu zuwa daga waje su yi sari. Bugu da kari akwai gidajen jama’a sama da dubu wadanda aka ce za a rushe, to ina ake so jama’a su sa kansu? Ni kaina tashi na yi na samu kaina a wannan kasuwa ita muka sani da ita muke cin abinci mafi yawancin matasan kasuwar sun yi karatu amma ba su dogara da gwamnati ba, sun zo suna neman na kansu suna samun rufin asiri, idan aka kore mu aka rushe ta jama’a da yawa za su shiga kunci. Don haka idan ya zama tilas su yi aiki a wajen da muke kasuwanci ya kamata su ba mu wani wurin ko su matsa da mu su ba mu wani kashi amma a ce za a tashe mu baki daya ba mu san inda za mu sanya kanmu ba, bai dace ba,” inji shi.

Alhaji Murtala Abubakar da ke sayar da kayan gwanjo a Kasuwar  Gatan-Kowa ya shaida wa Aminiya cewa da fari gwamnatin Jihar Legas ta shaida masu cewa za ta yi babbar hanya ce wacce za ta ratso ta gefen kasuwar lamarin da ya sa gwamnati yin rusau a gine-ginen da hanyar ta ratsa ta kansu. Wurare da dama an taba gine ginensu ba tare da an rushe su baki daya ba, amma abin mamaki da aka shigo cikin kasuwar da inda gidajen jama’a suke sai aka yi musu jan lamba da nufin su tashi baki daya.

“Ni kaina akwai gidana da nake zaune da iyalina an zo an sa jan fenti an ce, mu tattara kayanmu mu tashi cikin kwana bakwai, ina ake so mu sa kanmu? Yanzu haka akwai masu ’ya’ya 10 wadansu fin haka, in an kori mutane an rushe masu gidajensu ina ake so su sa kansu? Don haka ina kira ga gwamnatin Legas ta dube mu da idon rahama, ta sani mu ma ’yan kasa ne tamkar kowa kuma muna bada tamu gudunmawa a lokacin zabe,” inji shi.

Ya ce, tun lokacin da labarin rushe kasuwar ya zo suka shiga dimuwa inda wadansu ’yan kasuwar da dama ciwon hawan jininsu ya tashi. Don haka suke kira ga mahukunta su yi musu agaji.

Alhaji Isa Salahuddeen, dattijo ne da ke harkokinsa a kasuwar ya shaida wa Aminiya cewa, sun sami labarin gwamnatin Legas na yunkurin korarsu daga kasuwar ce domin ta dawo da ’yan kasuwar waya ta Computer Billage bangaren kasuwar tasu.

“Ban ga inda aka taba yin irin wannan ba, ta yaya za ka kori ’yan kasuwa daga wuri sannan ka kawo wadansu? Mu ba mu da mahimmanci ne ko mu ba ’yan kasa ba ne? Ya kamata gwamnati ta sauya manufa domin muna harkokinmu a nan fiye da shekara 40 bisa ka’ida, muna bai wa gwamnati hakkinta tun daga kan karamar hukuma. Don haka a ce za a kore mu ba tare da an ba mu wani wurin ba, sannan a bai wa wadansu namu wurin gaskiya wannan ba adalci ba ne,” inji shi.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto ’yan Kasuwar Gatan-Kowa, wacce ta samo sunanta daga Allah Gatan-Kowa, suna cikin zullumi da dar-dar kan matakin gwamnatin jihar na rushe kasuwar tare da korarsu baki daya ba tare da ba su wani wurin ba.