Sun sace uwargida madadin amarya a Zamfara
A kwanan nan ne wasu da ba a gane ko su wane ne ba, suka tafi gidan wani wani manajan gidan man fetur mai suna Sunusi Kalla Gumi da ke daki-Takwas a karamar Hukumar Gumi, Jihar Zamfara, suka dauke uwargidansa mai suna Hadiza da jaririnta dan wata uku, suka yi garkuwa da su sannan suka […]

A kwanan nan ne wasu da ba a gane ko su wane ne ba, suka tafi gidan wani wani manajan gidan man fetur mai suna Sunusi Kalla Gumi da ke daki-Takwas a karamar Hukumar Gumi, Jihar Zamfara, suka dauke uwargidansa mai suna Hadiza da jaririnta dan wata uku, suka yi garkuwa da su sannan suka bukaci a biya su diyyar Naira miliyan 30, kafin su sako su bisa zaton amaryar gidan ce.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, ita dai Hadiza, ita ce uwargida kuma su barayin suna neman amarya ce, wadda ’yar wani attaijiri ne mai suna Siddi daki-Takwas.
Majiyarmu ta ce barayin sun yi magana da mijin matar ta waya, inda suka ce sai ya ba su Naira miliyan 30 za su sako matar da jaririnta.
Wannan al’amari da ya tada wa jama’a da dama hankali, musamman mazauna daki- Takwas, kuma zuwa hada wannan rahoto ba a san halin da matar da jaririnta ke ciki ba. Kakakin ’Yan sandan Jihar Zamfara DSP Sanusi Amiru, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce suna nan suna gudanar da bincike a kai.
A wani labarin mai kama da wannan, jami’in ’yan sandan, a zantawarsa da manema labarai, ya ce rundunarsu ta samu nasarar kwato wasu mata biyu, Hajiya Hadiya Bello da Hajiya A’isha Amadu, wadanda suka fito daga karamar Hukumar Bukkuyum daga barayin da suka sace su kwanakin baya. Kamar yadda ya ce, wadanda suka sace su sun nemi a ba su Naira dubu 600.
Hakazalika rundunar ta samu nasarar kama wani mai suna Tukur Yahaya, da ake zargi da hada baki da shi a sace Hajiya Tumba da ke kauyen Kairo a karamar Hukumar Bukkuyum.