Sun sayi farcen roba na Naira dubu 16 ya koma irin na kare

Wata mata mai suna Serina Carmen da ’yar uwarta sun sayi farcen roba da kudinsa ya kai Fam 35 daidai da Naira dubu 16 da 800 da kwabo 26 don yi wa faratansu ado, amma daga bisani ba su samu biyan bukata ba, inda farcen ya koma irin na kare duk da cewa sun dauki […]

Sun sayi farcen roba na Naira dubu 16 ya koma irin na kare

Serina Carmen da ’yar uwarta

Wata mata mai suna Serina Carmen da ’yar uwarta sun sayi farcen roba da kudinsa ya kai Fam 35 daidai da Naira dubu 16 da 800 da kwabo 26 don yi wa faratansu ado, amma daga bisani ba su samu biyan bukata ba, inda farcen ya koma irin na kare duk da cewa sun dauki lokaci wajen yin tafiya a yi masu ado da faratan.

Mafi yawan masu bukatar a sanya musu farcen roba sun kaurace wa gidan ake yin adon, yanzu haka sun fara tunani za su fara sanya farcen roba da hannunsu maimakon amfani da inji da ake yi musu, ba a samu biyan bukata saboda faratan sun koma irin na karnuka.

Sai dai ba kowane lokaci ba ne ake samun irin wannan sakamako bayan sanya faratan robar ba.

Serina Carmen, mai shekara 25  da ’yar uwarta sun dauki lokaci don yin binciken a shafukan Intanet, wajen samun sabon salon adon da ya dace su yi wa faratansu  mai launin baki a jiki.

Serina Carmen da ’yar uwarta sun dauki hoton farcen da suka saya a birnin New York sannan suka kashe kudin da ya kai Dalar Amurka 45 daidai da Naira dubu 16 da 492 da kwabo 50.

Ma’aikatan sun yi aikinsu tukuru wajen gyaran faratan da yi musu ado, sai dai sun yi garajen dakatawa wajen ganin karshen sakamakon bukatarsu.

Serina ta ce: “Na nuna musu hotuna da launin abin da nake bukata daga cikin wayar salulata, sannan duk farashin da aka sanya musu a shirye suke su biya, koda kuwa karin kudi ne wajen kawata farcen.”

Bayan mai lura da injin sanya farcen ya dauki awanni, sai suka fahimci launin da aka yi akwai bambanci abin da suke bukata, musamman sauya launin farcen zuwa baki.

Ma’aikatan da suke aikin sanya farcen sun ce, suna fata zuwa wani lokaci faratan za su sauya.

Serina ta ce ba duka ba ne aikin bai yi kyau ba. ’Yar uwarta na alakanta adon faratan da cewa, adon da aka yi musu bai yi daidai da abin suka bada umarnin a yi musu ba.

Serina, ce ta yi sanadiyyar bata adon da aka yi shirin yi musu, saboda gaggawar a kammala cikin lokaci ya sa mai yin aikin ya yi garaje wajen gudanar da aikinsa.

“Duk da rashin kyan adon da aka yi wa farcen ba za ta iya cewa, ba ta bukatar adon ba, saboda ganin wahalar da wanda ya yi adon,” inji ta.

Bayan wallafa hoton faratan a shafin Facebook, dubban jama’a da dama sun yi ta rubuta martaninsu kan haka.

Ta ce: “Wani ya yi martanin cewa, faratan sun yi kama da na karnuka, kamar cirowa aka yi aka sanya, yayin da wadansu kuma suka ce, ba su ga dalilin biyan wadannan kudi ba don sayen faratan roba.”

Serina da ’yar uwarta sun shirya don yin fentin faratan su zama ababen sha’awa.