Sun shafe kwana 30 a kwance don lashe gasar wanda ya fi lalaci
Ana sa ran wani dan kasar Sabiya mai shekara 21 ne zai lashe gasar.
Wasu mutane a garin Brezna da ke kasar Montenegro sun shafe kwana 30 zuwa ranar 18 ga Satumban nan suna gudanar da gasar kwanciya a kan katifu domin lashe gasar “Mafi lalacin dan kasa” inda suka rusa tarihin da suka kafa a bara.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce, masu gasar sun kwanta na tsawon awa 117 a gasar da ta gudana a bara a wani wurin shakatawar a garin Brezna.
- Yadda aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna ke tafiyar hawainiya
- Ɗan bindiga ya sanya wa manoma haraji a ƙauyukan Katsina
Zuwa wancan rana sun kara kwana shida a kan kwana 24 a kan wadda suka yi, inda mutum biyar daga cikin bakwai da suke halartar gasar suka ci gaba da kwanciya a gado bisa fatan su lashe Yuro 1,000 ga duk wanda ya fi dadewa a kwance.
Ana sa ran wani dan kasar Sabiya mai shekara 21 ne zai lashe gasar.
“Gasa ce ta zuciya da tunani kuma masu halartarta suna da sha’awa a kanta,” mai shirya gasar, Radonja Blagojevic, wanda ya mallaki wurin shakatawar ya shaida wa manema labarai.
Ya kara da cewa: “Ayari ne mai ban sha’awa kuma za a samu abota da za ta ci gaba da gudana.”
An fara gasar ce a shekarar 2001 a Brezna don nishadantarwa tare da yin ba’a kan maganar da mutanen yankin Balkan ki yi cewa mutanen Montenegro malalata ne.
Akasarin wadanda suka shiga gasar sun fito ne daga kasar Montenegro, amma akwai wadanda suka fito daga kasashen Sabiya da Bosniya da Hazgobina da Kuroshiya da Rasha da kuma Yukrain.
Dokokin gasar sun nuna za a ajiye masu fafatawar a wani daki a wurin shakatawar, a rika ba su abinci sau uku a rana, kuma suna da ’yancin zuwa bayi bayan kowace awa takwas.
Ana kula da lafiyarsu, kawai abin da ake so, su kasance a kwance. Tsayuwa ko zama na iya sa a sallami mutum daga gasar.
“Daga farko muna da dokar babu tashi tsaye, koda zuwa bayi ne, don a ga wa zai fi dadewa a kwance. Amma a shekarar 2021, mun kawo sauyi cewa duk bayan awa takwas za su iya hutun zuwa bayi na minti 15,” in ji Blagojevic.
A tsohuwar kasar Yoguslabiya kabilu da dama sukan rika takala tare da yin jam’in ga mutane Montenegro da cewa malalata wadanda suka fi so su kasance a kan gado a kowane lokaci.
Wannan ne dalilin vullo da wannan gasa ta zakulo wanda zai fi dadewa a kwance don ba shi kyautar kudi.