Sun shayar da abokinsu ruwan batir a Inugu
Hukumar ‘yan sanda ta tsunduma cikin binciken wasu abokai da ake zargin sun shayar da abokinsu mai suna Sunday Onwe Uche ruwan batur a karamar hukumar Amuri Nkanu, a Inugu.Kakakin ‘yansandan jahar, Ebere Amaraizu ya tabbatar da faruwar wannan lamari inda yake cewa wanda ake zargi ya yaudari abokin nasa ne inda ya ba shi […]
Hukumar ‘yan sanda ta tsunduma cikin binciken wasu abokai da ake zargin sun shayar da abokinsu mai suna Sunday Onwe Uche ruwan batur a karamar hukumar Amuri Nkanu, a Inugu.
Kakakin ‘yansandan jahar, Ebere Amaraizu ya tabbatar da faruwar wannan lamari inda yake cewa wanda ake zargi ya yaudari abokin nasa ne inda ya ba shi ruwan batir din ya sha.
Kakakin ‘yansandan ya ce ana zargin cewa abokan sun dauki mutumin ne suka kai shi wani otal a Gariki Awkunanaw a garin Inugu daga nan ne suka dauke shi zuwa babbar hanyar Inugu zuwa Fatakwal, inda suka kwara masa ruwan batirin sannan suka tilasta masa ya sha.
“Lokacin da suka ba shi gubar ruwan batir din ya daure ya samu wani daga cikin dan uwansa ya ba shi labarin abin da ya faru. Ana zargin cewa akwai badakalar kudi a kan abin da ya faru. Kuma muna nan muna ci gaba da bincike a kan wadanda suka aikata wannn aika-aika. Shi kuma wanda suka zuba wa wannan guba ta ruwan batir yana nan da ransa a asibiti”.