Sun tono gawar mahaifinsu shekara 8 da binne ta don yin tsafi
Matasan sun tono gawar mahaifin nasu don yin tsafi da ita
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta tsare wasu matasa biyu, bisa zarginsu da tono gawar mahaifinsu da ya shekara takwas da rasuwa don yin tsafi da ita.
’Yan uwan junan biyu an gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin hada baki da kuma tono gawar mahaifin nasu.
- Mahara sun daka wawa kan dukiyoyin jama’a a kudancin Kaduna
- NFF ta kori Eguavoen bayan gaza zuwa Gasar Kofin Duniya
Mai gabatar da kara ya shaida wa alkalin kotun cewar, ’yan uwan junan sun gayyato wasu mutane wanda suka taimaka musu wajen tono gawar mahaifin nasu mai suna Zakarya Adekanye, wanda ya rasu tun a 2012, da nufin yin tsafi da gawarsa.
Sai dai matasan sun musanta zargin da ake tuhumarsu da shi a gaban kotun.
Alkalin kotun, Mohammed Adams, ya dage zaman kotun zuwa ranar 12 ga watan Afrilun 2022, sannan ya bayar da umarnin tsare matasan a gidan gyaran hali na Oke-Kura da ke Jihar.