Sun yanka jariri suka shanye jininsa
Dubun wadansu mutane hudu ya cika bayan da rundunar ’Yan Sandan jahar Kaduna ta cafke su bisa zargin kashe wani jariri sannan suka sha jininsa.A cewar rundunar ta ’Yan Sanda, wannan lamari ya auku ne a kwanakin baya a Hayin dan Mani da ke a karamar hukumar Igabi a jahar Kaduna.Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan jahar […]

Dubun wadansu mutane hudu ya cika bayan da rundunar ’Yan Sandan jahar Kaduna ta cafke su bisa zargin kashe wani jariri sannan suka sha jininsa.
A cewar rundunar ta ’Yan Sanda, wannan lamari ya auku ne a kwanakin baya a Hayin dan Mani da ke a karamar hukumar Igabi a jahar Kaduna.
Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan jahar Kaduna Sanusi Lemu ne ya gabatar da wadanda ake zargin a ranar juma’ar da ta gabata ga manema labarai a hedkwatar rundunar.
Ya ce za da zarar rundunar ta kammala bincikenta za ta mika su kotu.
daya daga cikin wadanda ake zargin mai Anas Hamisu, dan shekara kimanin 20, ya ce ba shi ne ya kashe jaririn ba, amma dai ya san lokacin da aka kwace jaririn daga hannun mahaifiyarsa.
“Ba ni na kashe jaririn ba kuma ba ni na kwato yaron ba, sai dai ina wajen lokacin da muka tafi tare da wani mai keke NAPEP, wanda shi ne ya kai mu gidan malamin da ya ce yana son a kawo masa jariri.
“Da suka fada min cewa malamin yana son a kai masa jariri sai gabana ya rika fadi domin ban san abin da zai yi da jariri ba. Daga nan sai shi mai Keke NAPEP din ya shiga wani gida kamar kango suka fito da wani abu kamar bindiga sannan muka tafi. Da misalin karfi 7 ne na yamma abin ya faru, an yi ruwan sama kuma mutane na cikin gidajensu . Sai suka shiga cikin wani gida suka kwato jariri a hannun wata mata, daga nan sai muka kai wa malamin jaririn. Da suka shiga da jaririn dakin malamin sai na ga sun fito da jini a kwarya. Aka ce wai mu sha, ni kuma sai na ce gaskiya ba zan sha jini ba. Da suka ga zan gudu sai suka danne ni da karfi suka dura min jinin. Bayan na sha ne sai na ji kaina ya fara ciwo kuma jikina ya canza, da na koma gida sai na fada wa babana abin da ya faru,’’ inji shi.
Ya ci gaba da cewa, shi mai Keke Napep din ya gudu, domin shi dama bai san shi ba.
Shi ma daya daga cikin matasan da ya ce an dura masa jinin ne da karfi mai suna Ibrahim Abubakar, ya bayyana yadda aka yi aka dura masa jinin.” Muna zaune ne da abokanmu sai na ce ba ni da lafiya, sai suka ce wai bari su kai ni wanjen malam ya ba ni maganin basir. Sai suka shiga dakinsa aka dauko jini aka ba ni wai maganin basir ne. Na ce ba zan sha ba, amma sai suka dura min da karfi,” inji shi.
Ya ce tun da ya sha jinin shi ma har zuwa lokacin da yake zantawa da Aminiya ba ya cikin hayyacinsa, domin bai taba shan jini ba sai da malamin da sauran abobakansa suka dura masa da karfi.
Sai dai kuma shi malamin mai Suna Mohammadu Sani Sulaiman, wanda ya kusa shekara hamsin, ya karyata zargin da ake masa cewa shi ya sa aka sato jariri aka kuma yanka shi.
A cewarsa, shi sana’arsa kasuwanci ne, amma bayan jarinsa ya karye sai ya koma malamta, inda mutane masu bukata suke zuwa wajensa yana yi masu addu’o’i da kuma taimako.” Ni ban san yaran nan ba, domin ni malamta nake yi a yanzu bayan jarina ya karye. Duk abin da suke fadi karya ne, domin ban sansu ba. Kuma ni ban kashe wani jariri ba ballantana in ba su jini su sha,” inji shi.
Haka shi ma makwabcin malamin mai suna Ahmadu Wamzam, wanda ake zarginsu tare da malamin wajen aikata wannan laifi, ya karyata cewa yana da hannu wajen sace jaririn. Ya ce bai san yaran ba, domin bai taba ganinsu ba sai a wannan rana da ’yan sanda suka je gidansa suka kama shi.
Shi kuwa mahaifin Anas Hamisu, Mai suna Muhammadu Hamisu Unguwar Sanusi, ya ce dansa ne ya fada masa abin da ya faru da shi a lokacin da ya je Unguwar Hayin danmani domin karbo sako a wajen yayar mahaifiyarsa.. “Yarona ne kuma mahaifiyarsa ta rasu, ya kan je wajen yayar mahaifiyarsa da ke Hayin danmani. Amma a wannan rana da ya dawo gida sai ban gane kansa ba. Sai na tambaye shi me ke faruwa, sai ya fada min cewa wadansu mutane ne suka dura masa jini ya sha bayan sun yanka jariri a gabansa. Daga nan ne sai na kai shi ofishin ‘Yan Sanda na fada musu abin da ke faruwa. Shi kuma jami’in ofishin (DPO) ya ce in bar shi ya kwana a hannunsu. Bayan ya dan natsu sai ya bayyana masu yadda abin ya faru. Da yadda ya ce mutanen suka danne shi suka dura masa jinin jaririn, da aka yanka ya sha,” inji shi.
Mahaifin yaron ya ce bai taba ganin malamin da sauran wadanda ake zargi ba sai a wannan rana da ‘yan sanda suka kama su. Sannan ya kuma yaba wa ‘yan sandan, inda ya ce ba su doki yaron nasa ba a lokacin da yake hannunsu.