Sun yi karar makwabta kan yawan carar zakara

Babu ranar da za mu zauna a gida mu ji shiru ba tare da jin carar zakaran ba.

Sun yi karar makwabta kan yawan carar zakara

Friedrich da matarsa, Jutta da suka kai makwancinsu kara saboda carar zakaranasa.

Wasu ma’aurata da suka tsufa a Jamus sun kai karar makwabtansu gaban kotu kan wani zakara mai yawan cara kusan sau 200 a rana, wanda hakan ya sa ba sa samun damar hutawa.

Friedrich-Wilhelm, mai shekara 76 da matarsa Jutta, ma’aurata ne daga garin Bad Salzuflen da ke Yammacin Jamus, sun yi ikirarin cewa babu ranar da za su zauna a gida su ji shiru ba tare da jin carar zakaran ‘Magda’ ba na makwabtansu.

Zakaran da ake zargin yana fara yin cara a kowace rana da misalin karfe 8 na safe, kuma ba ya tsayawa sai faduwar rana, inda masu shi za su zo su kulle shi da sauran kajinsu.

Shekara da shekaru suna kokarin tattaunawa da makwabtan game da carar zakaran, amma daga baya Friedrich da Jutta suka yanke shawarar kai su kotu don warware matsalar.

Friedrich-Wilhelm ya shaida wa manema labarai cewa, “Makwabcin ba ya barin zakaran ya saurara masu kuma dole ne mu rayu da carar ko kuma mu yi nasara a kotu.

“Ba za mu iya zama lambunmu ba kuma ba za mu iya bude kowace taga ba.

“Gaskiya ba za mu iya jurewa ba.

“Yana da wuya a iya kwatanta irin azabtarwar da muke sha,” kamar yadda matarsa Jutta ta shaida wa manema labarai.

Lauyan ma’auratan, mai suna Torsten Gieseke ya bayar da hujjar cewa, zakara mai yawan carar kamar Magda bai kamata ya kasance a cikin rukunin gidaje da ake bukatar shiru ba.

Mista Gieseke ya kara da cewa, carar zakaran ta tilasta wa wani makwabci yin hijira shekara biyu da suka gabata.

Rahoto ya ce, an kwatanta carar zakaran da kusan ma’aunin sautin ‘decibels 80’, kwatankwacin hayaniyar sautin babbar hanyar da ababen hawa ke wucewa ko ya yi daidai da gidan cin abinci mai cike da cinkoso.

Friedrich da Jutta sun gabatar carar zakara na yau da kullun da suka nada a matsayin shaida a gaban kotu, kuma sun yi ikirarin cewa, matakin da suka dauka na shari’a shi ne kawai zabin da suke da shi, bayan sun kasa yin magana da mamallakin zakaran.

Michael D, wanda ya mallaki zakaran ‘Magda’, ya shaida wa manema labarai cewa, zakara na taka muhimmiyar rawa a cikin garken kajinsa, domin yana samar da tsaro a tsakanin sauran tsuntsaye.

“Kaji suna bukatar zakara, in ba haka ba za su hadu da junansu ba,” inji shi.

Alkalin Kotun Gundumar Lemgo zai saurari karar Friedrich da Jutta nan ba da jimawa ba, domin ya yanke hukunci a kan makomar zakaran.

Abin sha’awa, wannan ba shi ne karo na farko da carar zakara ke haifar da shari’a a tsakanin makwabta ba.

A shekarar 2019, wani zakara mai suna Maurice ya dauki hankalin kafofin yada labarai na duniya, bayan carar da yake yi ta haifar da shari’a a tsakanin makwabtansu a Faransa

Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina

G-Fresh da Babiana sun nemi a saki Baɗejo

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa

Sojoji da dama sun ɓace bayan harin Boko Haram a Borno