Sun yi tir da manufofin gwamnati kan Jam’iyyar PDP da taron kasa
kungiyar Magoya Bayan Jam’iyyar PDP (PDP Core Supporters Network – PCSN), ta bayyana rashin gamsuwa da manufofin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan kan lamurran da suka shafi hadin kan jam’iyyar da kuma kwamitin taron kasa da aka kafa.Sakataren kungiyar PCSN ta kasa Injiniya Muhammad Eljamil Hashidu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya raba […]
kungiyar Magoya Bayan Jam’iyyar PDP (PDP Core Supporters Network – PCSN), ta bayyana rashin gamsuwa da manufofin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan kan lamurran da suka shafi hadin kan jam’iyyar da kuma kwamitin taron kasa da aka kafa.
Sakataren kungiyar PCSN ta kasa Injiniya Muhammad Eljamil Hashidu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Bauchi, inda ya ce kungiyar ta shawarci Shugaban kasa ya martaba tsarin mulkin jam’iyyar da kuma daukar kowane dan Najeriya a matsayin nasa ta hanyar watsi da manufofin wasu makusantansa da ke neman jawo rudani a kasar nan.
kungiyar ta nemi a gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi daga Jam’iyyar PDP, kuma ta soke rusa shugabannin jam’iyyar a jihohin Adamawa da Ribas da Kano, tare kuma da gaggauta korar Alhaji Bamanga Tukur daga shugabancin jam’iyyar don a samu hada kan magoya bayanta da bunkasa shugabancinta.
Eljamil Hashidu ya kara jawo hankalin Shugaba Jonathan kan a dauki matakin hukunta jami’an tsaron kasa da ’yan sanda da sojojin da aka samu da hannu wajen kisan Apo da sauran kashe-kashe da ake yi a kasar nan.
Haka ya shawarci Shugaban ya himmatu wajen kawo karshen matsalar yajin aikin malaman jami’a da ake fama da shi domin a samu inganta sashin ilimi.
Game da taron kasa kuma ya ce ba ya da wata fa’ida saboda duk abin da wannan kwamiti zai yi majalisun tarayya za su iya yi. Don haka ya ce taron na kunshe da wasu manufofi da su ne kurum suka sani tare kuma da niyyar kashe kudin kasa ba don amfanin jama’ar kasa ba.
Ya ce matsalar tsaro da ilimi da kiwon lafiya da hadurran da ke aukuwa su ya kamata a mayar da hankali ba taron da zai iya haifar da baraka a kasar nan ba. Don haka kungiyar ta ce a shirye suke idan ba a yi gyara ba cikin jam’iyyar za su koma gefen PDP da suka yi tawaye don a tafi da su kan hanyar kwarai.