Sun yi wa jami’an Hukumar Tace Fina-finai dukan kawo wuka

Hukumar Tace Fina-Finai Da dab’i ta Jihar Kano ta gurfanar da wasu mutane guda bakwai a gaban kotu bisa zarginsu da lakada wa ma’aikatan hukumar dukan kawo wuka a lokacin da suke bakin aiki a kasuwar Muhamamdu Abubakar Rimi. Tun da farko jami’an Hukumar Tace fina-finain ne suka kai wani samame a kasuwar, wadda da […]

Sun yi wa jami’an Hukumar Tace Fina-finai dukan kawo wuka
Sun yi wa jami’an Hukumar Tace Fina-finai dukan kawo wuka

Hukumar Tace Fina-Finai Da dab’i ta Jihar Kano ta gurfanar da wasu mutane guda bakwai a gaban kotu bisa zarginsu da lakada wa ma’aikatan hukumar dukan kawo wuka a lokacin da suke bakin aiki a kasuwar Muhamamdu Abubakar Rimi.

Tun da farko jami’an Hukumar Tace fina-finain ne suka kai wani samame a kasuwar, wadda da aka fi sani da Kasuwar Sabon Gari, a kan wasu masu sayar da maggunguna wadanda ke dauke da hotunan batsa a jiki.
Mai gabatar da kara, Anthony Edward ya shaida wa kotun cewa masu sayar da wadannan mutane da suka hada da Abdulalhi Adamu da Sulaiman Salisu da Aliyu Zakari da Abubkar dahiru da Sabi’u Jafar da Umar Sulaiman da Rilwanu Yusuf, sun ware kwanjinsu ne a kan ma’aikatan hukumar a lokacin da suka yi yunkurin kama magungunan da suke sayarwa, wadanda ke dauke da hotunan batsa. Hakan ya jawo jami’an Hukumar Tace Fina-finan ta sanar da ofishin ’yan sanda halin da ake ciki.
Daga nan ne hukumar ta shigar da kara kotu, inda aka tura dan sanda tare da masinjan kotu don kama su. Sai dai a nan ma ’yan kasuwar sun maimaita abin da suka yi a baya, inda suka dirar wa ma’aikatan da duka da kuma cin zarafi.
Lokacin da aka karanta musu laifinsu, dukkanin wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin; laifin da mai gabatar da kara ya ce ya saba da sashe na 155, 148, 267 da 327 na dokar finalkod.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Khalil Mahmud ya bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin a kurkuku tare da dage sauraren shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Nuwamba na bana.
A wani labarin makamancin wannan, hukumar ta gurfanar da wasu forudusoshi biyar a gaban kotun majistare mai lamba 11 da ke Nomanlan bisa zargin cewa sun fitar da fina-finansu ba tare da kai su gaban hukumar don tacewa ba.
Mutanen da ake zargin da fitar da wadansu fina-finai na fassarar Indiya zuwa Hausa sun hada da Abdulhadi Salman da Abduljalal Umar da Nura Jamilu da Abdullahi Maikaita da Sulaiman Jojo.
Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Khalil Mahmud ya bayar da umarnin daure wadanda ake zargin daurin watanni uku a kurkuku ko zabin biyan tarar Naira dubu 30. Haka kuma za su biya Hukumar Tace Fina-finai Naira dubu 20 ko kuma daurin watanni biyu a kan wahalar da ta yi na kamo su