Sun yi wa wata tsirara suka yada bidiyon a soshial midiya

Sun zuba mata barkono a al’aura kan zargin sata sannan suka yada bidiyon abin da suka yi a kafofin sada zumunta

Sun yi wa wata tsirara suka yada bidiyon a soshial midiya

An tsare wasu mata da suka tube wata tsirara suka zuba mata barkono a gabanta sannan suka yada bidiyon a kafofin sada zumunta.

Wadanda ake zargi su biyar sun kuma zuba barkono a al’aurar matar da suka yada bidiyon nata kan zargin ta saci wayar dayarsu a Jihar Edo.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Edo, Funsho Adeboye, ya ce bayan sun zargi matar da sata ne suka kira ta suka bukaci ta dawo da wayar.

Bayan ta dawo da wayar ne suka yaudare ta zuwa cikin gidan su mai wayar, inda suka lakada mata duka suka tube ta tsirara haihuwar uwarta sannan suka zuba mata barkono a gabanta.

Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin sun dauki bidiyon wannan danyen aiki da suka yi, wanda daga bisani suka yada a kafofin sada zumunta.

A cewarsa, dukkansu sun amsa lafiin da ake zargin su da aikatawa.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania