Sun yi zargin ana kwace gonakin ’yan Najeriya a iyakar Nijar
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gumel da Gagarawa Malam Sani Zoro ya ziyarci kauyen Jobi da ke karamar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa bayan da mutanen yankin suka yi zargin ana kwace musu gonakinsu a kauyen Kyalli da ke masarautar Dingas a Jamhuriyyar Nijar. Ana zargin sarakunan yankin Nijar da kwace gonakin makabtansu na Najeriya […]
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gumel da Gagarawa Malam Sani Zoro ya ziyarci kauyen Jobi da ke karamar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa bayan da mutanen yankin suka yi zargin ana kwace musu gonakinsu a kauyen Kyalli da ke masarautar Dingas a Jamhuriyyar Nijar.
Ana zargin sarakunan yankin Nijar da kwace gonakin makabtansu na Najeriya suna sayar wa masu dukiya, lamarin da ya jefa mutanen kauyen a mawuyacin halin rashin manomi.
Alhaji Sani Zoro ya ce ya kamata mutanen Nijar su fahimci cewa su ma suna da gidaje da gonaki a Najeriya, kuma babu wanda ya taba yi musu barazanar zai kwace su.
Ya ce, za su gabatar wa Gwamntin Tarayya rahoton halin da jama’ar garin Jobi suke ciki kuma za su bi duk matakan da suka kamata domin kwato wa jama’ar hakkinsu.
Da yake magana da yawun jama’ar garin Jobi, Malam Abdullahi danlami Jobi ya ce,
Sarkin Kasuwar Maigatari ne ke kai da kawo a tsakanin mahukuntan Nijar da na Maigatari don ganin ya raba su da gonakin, yana sa ana karbe gonakin nasu ana sayar wa mutanen Maigatari da Adare da Dirza da ke cikin kasar Dingas
Ya ce daga cikin gonakin da aka kwace musu har 83, wasu saye suka yi, wasu kuwa sun gada ne iyaye da kakanni, wasu kuma an ba su jinigina ne. Ya ce yayin da ake kwace gonakinsu da ke bangaren Nijar, su kuma mutanen Nijar din da ke da gonaki da gidaje a bangaren Najeriya babu wani mataki da hukumar Najeriya ta dauka a kansu.