Sun zama amarya da angon da suka fi tsufa a duniya
A ranar Asabar da ta gabata ne a kasar Birtaniya aka daura aure wani mutum, mai kimanin shekara 103 da amaryarsa, mai kimanin shekara 91, inda suka zama ango da amaryar da suka fi tsufa a fadin duniya. Angon mai suna, George Kirby da amaryarsa mai suna, Doreen Luckie, sun bayyana farin cikinsu don ganin […]
A ranar Asabar da ta gabata ne a kasar Birtaniya aka daura aure wani mutum, mai kimanin shekara 103 da amaryarsa, mai kimanin shekara 91, inda suka zama ango da amaryar da suka fi tsufa a fadin duniya.
Angon mai suna, George Kirby da amaryarsa mai suna, Doreen Luckie, sun bayyana farin cikinsu don ganin wannan ranar bayan da a cewarsu suka kwashe shekara 27 suna soyayya. An dai daura masu auren ne a gaban dimbin ’yan uwa da abokan arziki a wani otel da ke yankin kudancin kasar Ingila, kamar yadda kafar yada labarai ta Offbeat ta bayyana.
Jimullar shekarun su dai ya kama 194, wannan ya sa suka doke wasu Faransawa da suke rike da kambun amarya da angon da suka fi tsufa a duniya, wadanda jimullar shekarunsu suka kama 191.
Lokacin da yake zantawa da manema labarai, ango Doreen ya ce: “ba ya takaici ko kadan don auren ya zo a makare.”