Sun zargi Shugaban karamar Hukuma da maida sakatariyarta garinsu
Al’ummar garin Besse hedkwatar karamar Hukumar Koko-Besse da ke Jihar Kebbi sun zargi shugaban karamar hukumar Alhaji Buhari Aliyu danmasanin Koko da maida sakatariyar karamar hukumar zuwa garinsu, yayin da suka zargi jami’an karamar hukumar kan watsi da zuwa sakateriyarta domin gudanar da aikinsu.Wani ma’aikacin karamar hukumar mazaunin garin Besse da ya nemi a sakaya […]
Al’ummar garin Besse hedkwatar karamar Hukumar Koko-Besse da ke Jihar Kebbi sun zargi shugaban karamar hukumar Alhaji Buhari Aliyu danmasanin Koko da maida sakatariyar karamar hukumar zuwa garinsu, yayin da suka zargi jami’an karamar hukumar kan watsi da zuwa sakateriyarta domin gudanar da aikinsu.
Wani ma’aikacin karamar hukumar mazaunin garin Besse da ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana wa manema labarai cewa baya ga Sakataren karamar Hukumar da masinjoji da leburori babu wani mai zuwa wajen aiki.
Ya ce, shi kansa shugaban karamar hukumar ya maida sakateriyar karamar hukumar zuwa garinsu Koko, inda sai ya yi mako uku bai leka sakatariyar ba, ballantana sauran manyan jami’an karamar hukumar.
Majiyar ta ce tunda aka zabi shugaban karamar hukumar da kansilolinsa babu abin a zo a gani da suka gudanar don ci gaban al’ummar yankin, “shugaban karamar hukumar ya yi watsi da zuwa sakatariyar karamar hukuma, kullum idan mutun yana bakin titi yana ganin shugaban yana wucewa zuwa Birnin Kebbi,” inji majiyar.
Sai dai da Aminiya ta tuntubi shugaban karamar hukumar Alhaji Buhari Aliyu ya musanta wannan zargi, inda ya ce masu irin wannan zargi ba masu son ci gaban yankin ne ba, ba kuma gaskiya ba ne.
Ya ce lokacin da aka rantsar da shi ya yi taro da ma’aikatan karamar hukumar ya ja kunnensu kan zuwa wurin aiki da kuma yin aikin, kuma ya sa ka’idar kada wani ya kuskura ya kawo masa fayil a garinsu Koko ko kuma wurin da yake zama sai dai a ofis kawai.