Sun ziyarci jihohin Amurka 50 a kwana biyar

Mun ga abubuwan al’ajabi da yawa a lokacin tafiyar.

Sun ziyarci jihohin Amurka 50 a kwana biyar

Peter McConville da Abdullahi Salah da kuma Pavel Krechetove

Wasu abokan juna su uku, Peter McConville da Abdullahi Salah da kuma Pavel Krechetove, sun kafa tarihi bayan da suka ziyarci jihohi 50 na kasar Amurka a cikin kwana biyar.

Mutanen su uku sun fara ziyarar tasu ce daga yankin Vermont da nufin kafa tarihi, inda suka ziyarci jihohi 50 na kasar cikin kwana biyar da awa 16 da minti 20.

Da farko sun fara tafiyar ce a mota kafin daga baya su koma tafiya a jirgi, wanda suka fara daga Jihar Alaska sannan suka kare a Jihar Hawaii, inda suka shafe kwana biyar da awa 16 da minti 20.

McConville wanda shi ne ya jagoranci tafiyar, ya shaida wa gidan talabijin na KDAN-TV cewa “Ba zan iya bayyana irin abubuwan da muka gani ba saboda mun yi matukar gajiya.

­“Amma mun ga abubuwan al’ajabi da yawa a lokacin tafiyar.

“Tabbas akwai ababen mamaki da yawa.”

Kundin Tarihi na Duniya, ya dakatar da kafa tarihi a kan abin da ya shafi tsere ko tafiye-tafiye a 1996, saboda gudun kada a bai wa mutane kafar yin tukin ganganci da kasada, amma an sa McConville da abokansa cikin jerin mutanen da suka fi kafa tarihi game da abin da ya shafi tafiye-tafiye a duniya.