Sun ziyarci kasashe 19 a kwana guda
A makon jiya ne wasu mutum uku ’yan asalin kasar Norway sun kafa tarihi bayan da sun ziyarci kasashen nahiyar Turai har guda 19 a cikin sa’a 24, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta bayyana. Mutanen uku da sunayensu kamar haka: Gunnar Garfors da Tay-young Pak da kuma Øybind Djupbik, sun yi hakan […]
A makon jiya ne wasu mutum uku ’yan asalin kasar Norway sun kafa tarihi bayan da sun ziyarci kasashen nahiyar Turai har guda 19 a cikin sa’a 24, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta bayyana.
Mutanen uku da sunayensu kamar haka: Gunnar Garfors da Tay-young Pak da kuma Øybind Djupbik, sun yi hakan ne a cikin sa’o’i 23 da minti 40. Hakan yana nufin sun rusa bajintar da aka kafa a shekarar 2012, inda aka samu wani da ya yi irin wannan ziyarar, sai dai shi kasashe 17 kawai ya iya ziyarta.
Mafi yawan Turawan sun ce za su yi matukar farin ciki idan suka iya ziyartar kasashe 19 a tsawon rayuwarsu. Amma abin al’ajabi mutum ukun sun yi akan ne a kwana guda kacal.
Mutum ukun sun samun wannan nasarar ce ta hanayr daukar hayan motoci da shiga jiragen sama. Sun dai fara tafiyar ne da karfe 12 da wani abu na daren ranar Litinin din makon jiya daga kasar Girka. Daga nan sai suka nausa kasashen yankin Arewa-maso-Yammacin nahiyar wato: Bulgeriya da Macedoniya da Kosobo da Serbiya da Croatiya da Bosniya da Slobeniya da Austriya da Hungary da Slobakiya da Jamhuriyar Czech da Jamus da Netherlands da Belgium da Ludembourg da Faransa da Switzerland da kuma Liechtenstein.
Har ila yau, sun bayyana wa manema labarai cewa kasar da suka samu babban kalubale ita ce Kosobo. Inda akan iyakar shiga kasar suka tarar da layin jama’a mai tsawo. Sai suka yanke shawarar barin motarsu kuma suka ruga a guje, inda suka taka sayyadarsu a cikin kasar kafin su dawo su dauki motarsu. Sai kuma wani kalubale da suka fuskanta idan ’yan sanda suka tsare wani mai daukarsu hoto da suka tafi da shi. Jami’an sun tsare shi ne saboda laifin ya dauki hoto ba da izini ba a iyakar kasar da Bulgeriya. Daga nan sai suka ce “yayin da muka isa kasar Macedoniya ma mun fuskanci wata ’yar matsala, inda muka tarar motar da muka ce a ajiye mana kafin mu karaso, an bai wa wani.