Suna neman hana a hukunta wanda ya yi wa ’yarsa fyade

Bayan mahaifin yarinyar ya amsa cewa ya yi mata fyade sai suka hada baki suka nemi juya maganar

Suna neman hana a hukunta wanda ya yi wa ’yarsa fyade

‘Yan sanda

Iyalan yarinyar da mahaifinta ke lalata da ita sun zargi wani dan sanda da mai unguwa a Hayin Kwamanda Tsallaken Dogo Samaru da wata mata mai rajin kare hakkin dan Adam Malama Talatu Magaji Audu, da hada baki domin hana a kwato wa yarinyar hakkinta.

Mahaifin yarinyar da ake zargi da yi mata fyade, wanda ke zaune a anguwar Zariya, ma’aikaci ne a Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

“Ya shiga dakinmu da dare kowa ya kwanta a lokacin ya cire min kaya shi ma ya cire kayanshi, shi ne yake sa min gabana a gabanshi”, inji yariyar a zantawarta da Aminiya kan yadda mahaifin nata yake yi mata fyade da karfin tsiya.

Yarinyar da aka sakaya sunata ta ce ba sau daya mahaifin nata ya yi mata fyade ba kuma dukan ta yake yi idan ta nemi ta yi kururuwa.

Dangin yarinyar wadda auren mahaifanta ba sa tare sun ce bayan ya amsa laifinsa a ofishin ’yan Sanda na shiyyar Samaru, sai wadanda ake zargin suka nemi a yi sulhu ta hanyar yi wa yarinyar tayin kudi.

“Sai mu da DPO muka ki amincewa bayan nan sai shi DPO ya ba da umarni a tura mu Babban Ofishinsu da ke Kaduna, sai su suka hada baki suka karbo wata takarda da ke nuna cewa wai yana da ciwon tabin hakali”, inji masu zargin.

“Bayan sun kai anguwar Kawo [a Kaduna] sai [wanda ake zargin] ya fara yaga rigarsa tare da kartan kasa wai cewan sa ya tashi, nan da nan sai suka samo igiya suka yi mishi daurin goro.

“To daga nan sai shi dan sanda da aka hada baki da shi sai ya ce to ai tunda yana cikin wannan hali to ba za a iya karban shi ba, don haka za mu koma da shi Zariya, bayan mun dawo sai suka sake shi.

“Yazu haka yana nan yana yawonsa, kuma har yana cewa sai ya dauki mataki a kan ita yarinyar da dangisu”, inji masu zargin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kaduna, Muhammad Aliyu Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce duk abin da ya shafi maganar fyade ba a wasa da shi, saboda haka za su dauki mataki, kuma za su sa a sake kama wanda ake zargin a kara bincike.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7