Sunan Allah ya bayyana a jikin naman miya a Legas
Mutanen unguwar New Garage da ke yankin Oko-Oba a cikin karamar Hukumar Agege da ke Jihar Legas sun ga abin mamaki, yayin da aka gano sunan Allah a jikin naman miya a daya daga cikin gidajen Hausawan yankin.Mutumin da aka gano neman a gidansa wanda kuma mahauci ne da ke sana’a sayar da nama a […]
Mutanen unguwar New Garage da ke yankin Oko-Oba a cikin karamar Hukumar Agege da ke Jihar Legas sun ga abin mamaki, yayin da aka gano sunan Allah a jikin naman miya a daya daga cikin gidajen Hausawan yankin.
Mutumin da aka gano neman a gidansa wanda kuma mahauci ne da ke sana’a sayar da nama a kasuwar abbatuwa ta Oko-Oba, mai suna Adamu Abubakar ya bayyana cewa lamarin ya auku ne lokacin da ’ya’yansa suka sayo naman miya a kasuwa.
Ya ce: “A ranar Talatar da ta gabata yara sun sayo naman miya a kasuwar abbatuwa, bayan sun yanka naman sun zuba a tukunya za su tafasa sai kawai suka ga sunan Allah ya bayyana a cikin yanka biyar na naman. Sai aka buga mani waya aka sanar da ni sai na ce su cire neman daga wuta su ajiye, bayan na zo gida sai muka tabbatar da cewa sunan Allah ne. Mutane suka rika yin al’ajabi da lamarin. Akwai Yarabawan da suka rika neman a sayar musu Naira dubu daya amma na ki yarda.”
Malam Adamu wanda dan asalin Jihar Jigawa ne ya ce shi ne karo na farko da suka taba ganin sunan Allah a jikin nama.
“Duk shekarun da na yi ina aiki a abbatuwa, ban taba ganin sunan Allah a jikin nama ba, sai dai a ce an haifi saniya mai kai biyu amma a ce ga sunan Allah a jikin nama ban taba gani ba.” Inji shi.
Ya bayyana cewa ya tuntubi malamai da dama amma sun tabbatar masa cewa sunan Allah ne kuma za a iya ci.
An kwanakin baya an samu sunan Allah a jikin wani soyayyen nama a cikin unguwar Agege. Kuma an taba samun sunan Allah a jikin wata kankana a kasuwar kayan abinci ta Ilefo da ke Jihar Legas.