Sunayen Hausawa na gargajiya da ma’anarsu

Hakika harshen Hausa ya zama Hankaka mai da dan wani naka.

Sunayen Hausawa na gargajiya da ma’anarsu

Yadda Hausawa ke sarrafa harshe

Kimanin shekaru 40 da suka wuce, wata matar abokina ta haifi jariri, shi kuma ya yanke shawarar rada masa suna ‘Maikudi’.

Iyaye da danginsa da kuma matarsa suka ce atafau ba za a yi haka ba, saboda Maikudi ba suna ba ne.

Suka ja, shi ma ya ja, domin a cewarsa shi, bai ga laifin wannan suna ba na gargajiyar Bahaushe.

Kowa ya ja daga. Ana jibi za a yi bikin suna, sai ya hakura ya sake. Amma ba don yana so ba. Sai ya saka wa yaron suna Ibrahim.

Suna mai asali na Yahudu, wanda dukkanin addinain Yahudu da Kristanci da kuma Muslunci suke amfani da shi (Ibrahim na nufin Babankowa a asalin yaren).

Shi ke nan an wuce wurin, kowa na murna, sai daga baya aka ankara cewa sunan da ya sa na surukinsa ne. Kaka-kara-kaka.

Bisa al’adar Hausawa ba a kiran sunayen iyaye. Daga karshe, dole aka koma kiran jariri da Maikudi.

A yanzu dai jariri ya girma, ya kuma zama attajirin da ya tare kacokam a daya daga cikin manyan biranen Larabawa, kasancewarsa hamshakin dan kasuwa na kasa da kasa, inda yake cikin wadata. Wato dai ya amsa sunansa na Mai kudin.

Bayan ‘yan shekaru da faruwar wanccan al’amari, matar wannan aboki nawa ta sake haihuwa. Wannan karon ‘ya mace ce.

Sai ya kuduri aniniyar sa mata ‘Tabawa’. Nan ma aka sake kwata abin da ya faru a baya na kin sunan da yake so. Wannan karon ma dole ya hakura. Ya kuma sa mata suna Hajara, domin a zauna lafiya.

Hajara a tarihi mata ce ga Annabi Ibrahim, kuma sunan babbar yayarsu ce. Babu kuma yadda za a yi mahaifiyarsa ta kira wannan suna.

Domin a bisa al’adar Hausawa da kuma Fulani iyaye ba sa kiran sunan ‘ya’yansu na fari. Nan ma haka aka hakura aka ci gaba da kiran ta da ‘Tabawa’ sunan da ya ayyana tun farko.

A yanzu dai Tabawa malama ce a jami’a, tana kuma karatunta na zama Dakta, wato digirinta uku.

Ma’ana ta amsa sunanta, domin Tabawa na nufin uwar sa’a ko kuma wacce aka haifa a ranar Laraba (Talata a Kano da Katsina) wanda aka dauka ranar samun sa’a. (Shi ya sa ake ake yi wa ranar kirarin ‘Laraba Tabawa ranar samu’).

‘Ya’ya biyu wanda Allah Ya yi musu ludufi duk saboda sunayensu na gargjiyar Hausawa.

Shin ko mai ya sa muke kin sunayenmu na gargajiyar Hausawa?

Ba za mu sa wa ‘yanmu sunan ‘Mai wada’ ko ‘Goshi’ ko Jummare’ ko ‘Juma’ ba, amma za mu rada musu ‘Yasar‘ (attajiri- maikudi?) ko Fahad’ (Damisa) ko ‘Fawaz’ (mai nasara) ko kuma ‘Anwar (Haske).

Ba za ka rada wa ‘yarka ‘Tabawa’ ba amma za ka saka mata ‘Mahjuba (Lullubabbiya) ko ‘Samira (ma abociyar hirar dare – ‘yar Tik tok?) ba.

Idan ka rada wa ‘yarka ‘Dare’ ka shiga uku. Amma in ka saka mata ‘Laila’ (dare da larabci) shi ke nan ka burge, duk da abu daya ne bambancin kawai Larabci.

Mafi yawan sunayen da Hausawa kuma Musalmai ke rada wa ‘ya’yansu a yanzu, ba su da wata alaka da musulunci.

Kuma yawancin Hausawan da ke amsa sunayensu na larabcin ba su san ma’anarsu ba.

Sunaye irin su Zillaziyya, Nakashibandiyya, Naja’atu, ‘Adawiya’ da sauransu na larabawa ne muka ara, muka kuma yafa, yanzu kuma muke kakaba su a kanmu a dabia’armu ta kyamar duk wani abu da ya shafi gargjiyar Hausawa ko da ba shi wata alaka ta kusa ko ta nesa da addini.

La’akari da wadannan abubuwa ta sa ni da abokina (baban Tabawa da Maikudi) da na baku labari, muka yanke shawarar yin wani abu dangane da wannan lamari na sunayen Bahaushe na gargajiya, muka kuma samu daukin wani abokinmu wanda ya dauki wannan al’amari da azama ya shiga tattara sunayen Hausawa na gargajiya wadanda kuma ba su da alaka da maguzanci.

Sunaye irin su ‘Abarshi’ an samo shi ne daga addu’ar “Allah Ya bar shi’, mace kuma ‘Abarta’.

Bahaushe na saka wannan suna ne ga jaririn da aka haifa bayan bari da mahaifiyarsa ta yi a baya kafin ta haife shi.

Daga cikin wadannan sunaye akwai Mantau, Ajefas, Barmani, Ajuji da kuma Barau. Kun ji yadda fitacciyar mai kidan kwaryar nan ‘yar asalin Katsina Barmani Choge ta samo sunanta.

Sunan Shekarau daga kalmar shekara aka samo shi. Bahaushe yana kiran jaririn da da ya dade a cikin mahaifiyarsa har zuwa shekara ko kuma fiye da wannan suna, inda mace kuma ake kiran ta Shekara.

Kun ji yadda tsohon gwamnan Kano kuma Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya samo sunansa.

Tanko shi kuma na nufin wanda ya biyo ‘ya’ya mata uku a haihuwa.

Haka kuma wannan suna daidai yake da Gudaji, Tankari, Yuguda, Iguda’, Guda.

Ga inda Gudaji Kazure dan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa da kuma tsohon gwamnan Jihar Bauchi Isa Iguda suka samo asali.

A da, jariri mai suna Anini na nufin yaron bawa ne, kasancewar anini kudi ne da ke nuna mallaka. Amma da zuwan Turawa da kuma kawar da bauta Anini sai ya koma yana nufin dan da aka haifa da kananan gabobi.

Hakika harshen Hausa ya zama “Hankaka mai da dan wani naka” domin hatta sunaye na musulunci Bahaushe ya Hausantar da su kamar haka: Guruza, Ahmadu ke nan.

Da’u, Dauda ne, Gagare kuma Abubakar. Auwa, Hauwa ce. Daso kuma Maryam ke nan, Babuga Umar ne. Ilu, Ila, Sama duk Isma’il ake nufi.

Ga mai sha’awar sannin wadannan sunaye sai ya je shiga wannan rariyar ta intanet https://bit.ly/42HJl97