Sunayen unguwannin da Wike zai yi rusau a Abuja
Hukumar Birnin Tarayya ta fitar da sunayen unguwanni da gine-gine 6,000 da Minista Wike zai yi rusau
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince a rusa gine-gine sama da 6,000 a yankunan Garki da Jabi da wasu unguwanni 28 da suka saɓa da tsarin birnin tarayyan ba.
Hukumar kula da birnin tarayyar (FCTA) ta fitar da jerin sunayen unguwannin, inda ta bayyana cewa gine-ginen ta riga aka sanya wa alama ne rusau din zai shafa, a shirin gwamnati na kawar da gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a birnin.
Ga jerin unguwannin da abin zai shafa:
- Apo Mechanic Village
- Byanzhin.
- Dawaki.
- Dai Dai.
- Durumi.
- Dutse.
- Garki.
- Garki Village.
- Gishiri.
- Gwagwalada.
- Idu.
- Jabi.
- Kauyen Kado.
- Karmo.
- Karshi.
- Karu.
- Katampe.
- Kauyen Ketti.
- Kpaduma.
- Kabusa.
- Kauyen Kpana.
- Kubwa.
- Lokogoma.
- Lugbe.
- Mabushi.
- Mpape.
- Nyanya.
- Piya Kasa.
- Jikwoyi
- Galadima
Tun ranar Litinin da aka rantsar da tsohon gwamnan na jihar Ribas a matsayin Minista, ya sha alwashin dawo da birnin kan ainihin taswirarsa, ruguza gine-ginen aka yi ba bisa tsaru ba, da kuma kawo karshen badaƙalar filaye a babban birnin.
Wike wanda ya ce ya zaga birnin Abuja a cikin dare domin ya ga al’amura da kansa, ya koka bisa yadda aka yi gine-gine a filayen da gwamnati ta kebe ba don ginawa ba.
Ya ce: “Za mu kwace duk filayen da masu su ba su gina ba, don haka dole masu su su ci gaba da aiki nan take.
Sai dai daraktan sashen kula da ci gaban FCTA, Muktar Galadima ya ce za a gudanar da wani sabon bincike.