Super Eagles sun baro Libya bayan shafe sa’o’i 14 a tsare

‘Yan wasan sun shafe sa’o’i 14 a filin jirgin saman kafin samun iznin tashi zuwa Najeriya.

Super Eagles sun baro Libya bayan shafe sa’o’i 14 a tsare

Bayan shafe sa’o’i sama da 14 a filin jirgin sama na Al Abraq, Gwamnatin Libiya ta bai wa jirgin Najeriya izinin tashi domin dow da tawagar ’yan wasan Super Eagles zuwa gida.

Ɗan jaridar wasanni Adepoju Tobi Samuel, wanda aka fi sani da OgaNlaMedia, ne ya bayyana hakan.

Ya ce: “Bayan matsin lamba daga wurare daban-daban, Gwamnatin Libiya ta amince ta bai wa jirgin ValueJet izinin tashi domin dawowa gida Najeriya.

“Sun yi ƙoƙarin cewa sai mun fara sauka a Benghazi kafin mu tafi Najeriya, amma NFF ta dage cewa dole ne a bayar da izinin tashi daga filin jirgin Al-Abraq zuwa Najeriya.”

Wani ɗan wasan Super Eagles, Bruno Onyemaechi, shi ma ya tabbatar da labarin, inda ya ce, “Ni da Libiya, mun yi hannun riga. Babu abin da zai haɗa ni da ku. Alhamdulillah ina hanyar komawa gida.”

An zargi hukumomin Libiya da ƙin bai wa jirgin Super Eagles, ValueJet izinin dawo da ’yan wasan Super Eagles zuwa Najeriya.

Hakan ne ya sanya hukumomi a Najeriya suka yi kira da kakkausar murya don ganin an bar ’yan wasan sun dawo gida lafiya.

Tun da farko tawagar Super Eagles za ta kara da ƙasar Libya a wasan neman gurbin Gasar Kofin Afrika.

Da isar jirginsu Benghazi aka sauya akalarsa zuwa Al Abraq, inda suka shafe sa’o’i sama da 14 a tsare, babu abinci ko ko masauki ko layin intanet.

An zargi hukumomin Libya da yin hakan a matsayin wani salo na karya lagon tawagar ta Najeriya a wasan da kasashen biyu za su fafata na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON).

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Libya ta fitar da sanarwa tare da bayyana takaicinta bisa abin da ya faru.

A cewarta, rashin kyan yanayi ne ya sa aka karkata akalar jirgin Super Eagles Zuwa Al Abraq, kuma hakan abu ne da ke iya faruwa da kowa a kowane lokaci, kamar yadda a baya ya faru da tawagar ‘yan wasan kasar lokacin da suka zo Najeriya buga zagayen farko na wasan.

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos

Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda