Super Eagles sun iso Najeriya bayan shiga tsaka mai wuya a Libya

’Yan wasan sun sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da yammacin ranar Litinin.

Super Eagles sun iso Najeriya bayan shiga tsaka mai wuya a Libya

Tawagar ’yan wasan ƙwallon ƙafa na Super Eagles sun iso Najeriya bayan shafe sama da sa’o’i a filin jirgin sama na Al Abraq da ke ƙasar Libya.

’Yan wasan sun sauka a filin jigrin saman Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Litinin.

’Yan wasan sun shafe tsawon sa’o’i a filin jirgin saman ba tare da samun matsuguni ko abincin da za su ci ba.

Lamarin dai ya haifar da ruɗani a tsakanin hukumomin Najeriya da Libya.

Hakan ne ya sanya Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, gayyatar Jakadan Libya a Najeriya domin jin ba’asin abin da ya faru.

Daga bisani Gwamnatin Libya ta bai wa jirgin Najeriya damar barin filin jirgin saman domin dawowa gida da ’yan wasan.

Kyaftin ɗin tawagar, William Troost-Ekong, ya ce wallafa a shafinsa cewar sun dawo gida lafiya.

“Mun dawo gida lafiya. Ina alfahari da wannan tawaga, ba za a iya karya lagon ’yan Najeriya ba. A cikin jininmu yake shawo kan matsala.”

Shi kuma ɗan wasan gaban Leverkusen, Victor Boniface, ya wallafa cewar “Mun dawo Najeriya.”

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025