…Super Eagles ta sha kashi a hannun Uganda

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ta sha kashi a wajen kungiyar kwallon kafa ta Uganda da ci 1-0. An gudanar da wasan ne a Uyo da ke Jihar Akwa-Ibom inda ’yan kallo da dama suka nuna takaici da mamakin ganin yadda Uganda ta bi Najeriya har gida ta zura […]

…Super Eagles ta sha kashi a hannun Uganda
…Super Eagles ta sha kashi a hannun Uganda

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ta sha kashi a wajen kungiyar kwallon kafa ta Uganda da ci 1-0.

An gudanar da wasan ne a Uyo da ke Jihar Akwa-Ibom inda ’yan kallo da dama suka nuna takaici da mamakin ganin yadda Uganda ta bi Najeriya har gida ta zura mata kwallo daya mai ban haushi a raga ba tare da ta fanshe ba.
Jim kadan bayan an tashi wasan ne sai magoya bayan Super Eagles suka nuna bacin ransu kuma suka nuna shakku a kan ko kungiyar za ta iya tabuka abin kirki a nan gaba.Wasu sun bayyana ra’ayinsu a kan cewa gwamma a maye gurbin daukacin ’yan kwallon da na Flying Eagles wadanda suka lashe gasar cin kofin matasa na Afirka a karo na 7 a makon jiya.
Daniel Amomachi ne ya jagoranci kungiyar a wasan, sai dai ya zuwa shekaranjiya Laraba Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayar da umarnin a sabunta kwantaragin tsohon kocin kungiyar, Stephen Keshi.