Super Falcons za ta samu horo a Kanad
Babbar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya da aka fi sani da Super Falcons a ranar 19 ga watan Mayun gobe ne za ta tafi Toronto da ke Kanada don yin atisaye a shirye-shiryen halartar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da za a fara a ranar 6 ga Yunin wannan […]
Babbar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya da aka fi sani da Super Falcons a ranar 19 ga watan Mayun gobe ne za ta tafi Toronto da ke Kanada don yin atisaye a shirye-shiryen halartar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da za a fara a ranar 6 ga Yunin wannan shekara.
Kamar yadda kafar sadarwar wasanni ta AfricanFootball.com ta kalato, kungiyar za ta fafata a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata ne a rukunin da suka hada da kasashen Sweden da Australiya da kuma Amurka.
Haka kuma wannan ziyara da kungiyar za ta kai Kanada tamkar wani yunkurin ne a shirin tunkarar gasar Olamfik ta 2016 inda Najeriya za ta hadu da Mali a ranar 9 ga Mayun wannan shekara a gasar neman hayewa gasar.
Idan za a tuna kungiyar Falcons ta lallasa Mali da ci 9-1 a gasar a wasan karshe na neman hayewa gasar wasanni ta Afirka watau (All Afircan Games) da zai gudana a Congo-Brazzabille