Surajo Mai Asharalle ya rasu

Alhaji Surajo ya yi fice a wajen waƙar Hausar nan da ake kira Asharalle.

Surajo Mai Asharalle ya rasu

A daren ranar Alhamis Allah Ya yi wa shahararren mawaƙin Asharalle na Katsina, Alhaji Surajo mai Asharalle rasuwa a asibitin koyarwa na Gwamnatin tarayya da ke Katsina bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita.

Alhaji Surajo ya yi fice a wajen waƙar Hausar nan da ake kira Asharalle.

Daga cikin irin waƙoƙin shi da suka yi fice baya ga mai taken Asharalle sai kuma wadda ya yi mai taken ‘Ta yi rawa ɗakin ba kowa’.

Marigayin ɗan asalin yankin masarautar Tsanni ta ƙaramar hukumar ɓatagarawa, mawaƙin ya yi waƙoƙi da dama musamman a wajen shagalin bukukuwan aure, naɗin sarauta ko wani babban taron da aka kira shi don nishaɗantar da al’umma.

Shi ne mawaƙin da marigayi Dokta Mamman Shata ya naɗa a matsayin Garkuwan shi a fagen waƙa.

Har ila yau, Alhaji Surajo shi ne, Farautan Katsina wato, shugaban masu farauta na Katsina. An yi jana’izarsa a yau Juma’a da safe a gidan shi da ke ƙofar ƙaura.

Ya rasu ya bar mata da yara da sauran danginsa.