Surukin Sanata Goje ya koma ɓangaren Gwamna Inuwa
Dasuƙi, wanda ke auren Zainab, ’yar Goje ta biyu, na hannun daman tsohon gwamnan ne, wanda ya kasance Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu kuma Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi (ALGON) a zamanin mulkin Goje.
Ibrahim Dasuƙi Jalo Waziri, surukin tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Sanata Ɗanjuma Goje, ya juya wa tsohon uban gidan nasa baya, yana mai jaddada cikakken goyon bayansa ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ke zaman doya da manja da tsohon gwamnan.
Dasuƙi, wanda ke auren Zainab, ’yar Sanata Goje ta biyu, na hannun daman tsohon gwamnan ne, wanda ya kasance Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu kuma Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi (ALGON) a zamanin mulkin Goje.
A baya-bayan nan, Sanata Ɗanjuma Goje da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, waɗanda ake wa kallon manyan jiga-jigan siyasar Gombe, sun sa zare kan tsayar da ɗan takarar kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya, wadda tsohon gwamnan ke neman komawa a karo na biyar.
A yayin taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC domin fitar da ’yan takarar sulhu gabanin zaɓen 2027, wanda Gwamna Inuwa ya jagoranta, shi da masu ruwa da tsaki sun zaɓi Muhammad Ahmed Deba, a matsayin wanda suka fi so ya zaman ɗan takara na sasanci.
- Yadda za a kayar da Tinubu cikin sauƙi a 2027 — Buba Galadima
- Kano: An kashe mutum 5 a sabon hari a Tsanyawa
- APC ta sahale wa Sanata Goje neman takara
Sai dai kuma Sanata Goje ya ƙalubalanci matakin, kuma daga ƙarshe ya samu tantancewa daga uwar jam’iyyar APC domin shiga zaɓen fid-da-gwani na ɗan takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya, da za a gudanar.
Amma, surukinsa, Ibrahim Dasuƙi Jalo kuma tsohon Kwamishinansa, ya bayyana goyon baya ga Gwamna Inuwa, yana mai yaba salon shugabancin gwamnan, da ya ce ta samu gagarumar nasara a fannoni daban-daban.
A cewarsa, ayyukan raya ƙasa da gwamnatin ke gudanarwa musamman a ɓangarorin samar da ababen more rayuwa, tabbatar da zaman lafiya da haɗa kan al’umma sun kara wa jama’a ƙwarin gwiwa da amincewa da gwamnati.
Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Harkokin Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, Dasuƙi Waziri ya ce salon shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya ya taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a cikin Jam’iyyar APC da ma jihar baki daya.
“Mun gamsu da irin ci-gaban da ake samu ƙarƙashin wannan gwamnati. Gwamnan ya nuna jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci-gaban al’umma,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da bai wa gwamnatin goyon baya domin tabbatar da ɗorewar hadin kai da ci-gaban jihar.
Da yake mayar da martani, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yaba da ziyarar tare da bayyana ta a matsayin wata alama ta dattaku na siyasa da kishin ci-gaban jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye domin inganta walwala da ci gaba a dukkan sassan jihar.