Sweden ta amince a ƙona Alƙur’ani ranar Sallah

Rundunar ƴan sandan Sweden ta bada izinin gudanar da taron ƙona Alƙur’ani a gaban wani masallaci dake Stockholm babban birnin ƙasar  ranar Sallah Babba. Jerin zanga-zangar adawa da Musulunci da kuma tarrukan  ƙona Alƙur’ani da ake yi a Sweden sun jawo saɓani tsakaninsu ga Turkiyya, inda ta tara mata hanyar shiga ƙungiyar ƙawance ta NATO. […]

Sweden ta amince a ƙona Alƙur’ani ranar Sallah

Mazu zanga-zangar kona Al-Kur’ani a Sweden

Rundunar ƴan sandan Sweden ta bada izinin gudanar da taron ƙona Alƙur’ani a gaban wani masallaci dake Stockholm babban birnin ƙasar  ranar Sallah Babba.

Jerin zanga-zangar adawa da Musulunci da kuma tarrukan  ƙona Alƙur’ani da ake yi a Sweden sun jawo saɓani tsakaninsu ga Turkiyya, inda ta tara mata hanyar shiga ƙungiyar ƙawance ta NATO.

A baya bayan nan dai ƴan sandan Sweden sun ƙi bada izinin shirya taron ƙona Alƙur’ani, amma kotunan ƙasar sun ce hakan ya saɓa da haƙƙin faɗin albarkacin baki.

Jima’i ya zama wasan motsa jiki, za a yi gasar fidda gwaninsa a Sweden

Kona Alkur’ani a Sweden ya jawo Allah-wadai daga kasashen Musulmai 

Wani ɗan gudun hijirar Iraƙi mai fafutukar haramta karanta Alƙur’ani a Sweden, Salwan Momika ne ya shirya taron.

A watan Janairun bana dai Turkiyya ta dakatar da tattaunawa da Sweden game da ƙudirinta na shiga ƙungiyar NATO bayan da shugaban jam’iyyar ƴan ra’ayin riƙau ta Denmark, Rasmus Paludan ya ƙona Alƙur’ani a kusa da ofishin jakadancin Turkiyya dake Stockholm.

Haka kuma ƙasashen Musulmi da dama irin su Saudiyya, Jordan, da Kuwait sun yi tur da ƙona Alƙur’anin da aka yi a watan Janairun.

A ranar Laraban nan dai Firaministan Sweden, Ulf Kristersson ya ce har yanzu ƙasarsa na fatan shiga NATO kafin taronta na watan gobe amma ba ya jin hakan za ta samu.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan