Switch na tura kudade zuwa Najeriya kyauta a wannan Kirsimeti

…domin ’yan Najeriya mazauna Birtaniya, Amurka da Kanada

Switch na tura kudade zuwa Najeriya kyauta a wannan Kirsimeti

Dama ta samu ga ’yan Najeriya da ke Amurka, Birtaniya da Kanada na tura kudi zuwa gida kyauta a Kirsimetin bana ta tsarin Switch na tura kudi daga wata kasa zuwa wata.

Wata dama ce ta musamman ga masu amfani da manhajar Switch su tura kudade a Naira, Dala, Fam ko Yuro, ba tare da an caje su ba, muddin mai turawa da mai karbar kudin na amfani ne da manhajar Switch.

Kafar da bankin Sterling Bank ya samar wani sabon cigaba ne da ya samar da damar tura kudade zuwa Najeriya daga wasu kasashe.

Da yake bayyana hakan, Shugaban Sashen Huldar Bankin Dillalai da Kwastomomi na Sterling Bank, Shina Atilola, ya shawarci ’yan da ke kasashen waje su yi amfani da sabuwar kafar ta Switch wurin tura kudade ga ’yan uwansu da ke gida Najeriya a lokacin Kirsimeti, don ba za a caje su ko sisi don sun tura kudadaen ba.

Atilola ya ce, “Lokacin da ’yan Najeriya mazauna waje ba sa iya amfani da katin cirar kudinsu su tura kudi zuwa asusun bankinsu na gida kudi saboda tsadar cajin da bankuna ke musu ya wuce.

“Switch ya saukaka tura kudade ga ’yan uwa da ke Najeriya, ya kuma saukaka yin cinikayya ta intanet ga masu amfani da shi a Najeriya.

“Yana da matukar amfani ga ’yan Najeriya mazauna Birtaniya, Amurka da Kanada da ke son su tura wa ’yan uwansu da ke gida kudade a lokacin Kirsimeti.

“Za su iya yin hakan ta hanyar bude asusun Switch domin su samu damar tura kudade ga ’yan uwansu da ke amfani da Switch kyauta.”

Ya ce Switch da na tsarin ‘Funding with Card’ wanda ta nan masu amfani da manhajar za su iya tura kudi zuwa asusunsu na Naira ko da kuwa da kudaden wasu kasashe ne.

Atilola ya ce masu amfani da manhajar Switch ko shafinsa na intanet na iya sanya kudade a asusun na Switch ta hanyar tura kudade daga asususun bankinsu na gida ko daga wata kasa zuwa wata.

Za kuma su iya sanya kudade a cikin asusun nasu ta kamfanonin tura kudade tsakanin kasashe masu yin hakan.

Ba a cazar wanda aka tura wa kudi, amma bankin da ke tura kudin na iya sanya caji saboda aikin da ya yi.

Ana iya amfani da Switch ta shafinsa na intanet ko a sauke manhajarsa ta na’urorin Android da IOS.

Ana amfani da switch domin huldar kudade nay au da kullum da suka hada da biyan kudade, tura kudi, neman biya, zuba jari, da kuma inshora da dangoginsu kamar yadda ya yi bayani.

“Switch ya samar wa kwastomomi karin fa’idoji na rance, zuba jari da inshora cikin sauki ta hanyar hadaka,” inji shi.

An tsara Switch ne domin biyan bukatar kwastomomi na gina nagartacciayr rayuwa ta kudi da kuma ta nan gaba domin biyan bukatu daban-daban ta hanya daya cikin sauki tare da bayar da zabin tsarin sarrafa kudin.

Jami’in bankin ya kara da cewa Switch zai share wa kwastomomi hawaye na neman saukin hulda da banki da zai ba da karin dama ta samun rance, kudaden shiga, zuba jari da kuma inshora domin samun kariya daga tsautsayi.

Switch na da hanyoyin amfani da dama kuma ya samu amincewar Babban Bankin Najeriya (CBN) sannan yana da inshora da Hukumar Inshorar Ajiya ta Najeriya (NDIC).

Sabon tsarin dama ce ga ’yan Najeriya mazauna ketare su amfana ta sha’anin banki da dangoginsa cikin sauki da kwarin gwiwa ba tare da wata tangarda ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos