Sylva ya zama dan takarar gwamnan Bayelsa a APC

A yanzu Sylva zai kara da gwamna mai ci, Sanata Douye Diri.

Sylva ya zama dan takarar gwamnan Bayelsa a APC

Tsohon Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan Jihar Bayelsa a jam’iyyar APC.

Sylva, wanda tsohon gwamna ne da ya mulki jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012, ya samu kuri’u 52, 061 inda ya doke wasu ‘yan takara biyar ciki har da dan takarar gwamna na jam’iyyar a 2019, Cif David Lyon.

Da wannan sakamakon, a yanzu Sylva zai kara da gwamna mai ci, Sanata Douye Diri wanda a farkon makon ya zama dan takarar jam’iyyar PDP.

Da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Asabar a Sakatariyar jam’iyyar APC da ke Yenagoa, Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwani na jam’iyyar APC na Jihar Bayelsa, Manjo Janar A. T. Jibrin (mai ritaya), ya ce an gudanar da zaben cikin lumana a ranar Juma’a a fadin jihar.

Ya sanar da kuri’un da sauran manema takarar suka samu da suka hada da Cif Festus mai kuri’u 1591, sai Daumiebi ya samu kuri’u 557, inda Joshua Maciver ya samu kuri’u 1277.

Joshua Maciver ya samu kuri’u 2078 yayin da Ogbomade Johnson ya samu kuri’u 584.

Ya ce kwamitin ya yi aiki ne da umarnin da shugabannin jam’iyyar na kasa suka ba su na gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar gabanin zaben gwamnan da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ya ce duk da cewa yanayin da jihar ke fama da shi ya kawo tsaiko wajen kammala aikin, amma sun samu damar gudanar da zaben fidda gwanin da masu neman takara da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka amince da shi.

’Yan takara biyu, Ongoebi Etebu Maureen da Joshua Maciver, sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin, inda suka yi alkawarin yin aiki domin samun nasarar jam’iyyar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

A makonnin bayan nan ne dai Mista Sylva ya yi murabus daga mukaminsa a kasar domin neman sabon wa’adi a matsayin gwamnan Jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a yankin Neja Delta.

Murabus din Sylva ya zo ne kwanaki 60 kacal, kafin wa’adinsa a kan mukamin Karamin Ministan Albarkatun Mai ya kare kuma a daidai lokacin da ake shirin kafa sabuwar gwamnati a Najeriya, inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke makonninsa na karshe a kan karagar mulki kafin ya mika wa zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

Idan ana iya tunawa, a watan Agustar shekarar 2019 ne aka nada Sylva a matsayin karamin ministan albarkatun man fetur, inda ya jagoranci manyan sauye-sauye a fannin mai wadanda suka hada da zartar da dokokin da suka yi wa tsarin kasafin kudin sashen kwaskwarima a wani yunkuri na karfafa zuba jari.

A lokacin da yake rike da mukamin minista ne aka ga raguwa matuka a yawan man da Najeriya ke hakowa a cikin shekaru da dama da suka gabata, sakamakon satar danyen mai da fasa bututu da wasu baragurbin mutane ke yi.

Daga bisani kasar Angola ta zarce Najeriya a matsayin kasar da ta fi fitar da man fetur a nahiyar Afirka na wasu watanni a bara.