T. Y. Danjuma: Babu dattako cikin kalaman ‘Dattijo’

A lokacin da aka ce kasa kamar Najeriya mai dauke da kabilu mabambanta sama da 300, mai al’umma mabiya addinai daban-daban, za a samu tsoho dan shekara 80 yana kiran kabilarsa ta dauki makami ta yaki wasu al’ummu na daban, babu shakka akwai matsala gagaruma. A wannan makon, GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci ne game […]

T. Y. Danjuma: Babu dattako cikin kalaman ‘Dattijo’

A lokacin da aka ce kasa kamar Najeriya mai dauke da kabilu mabambanta sama da 300, mai al’umma mabiya addinai daban-daban, za a samu tsoho dan shekara 80 yana kiran kabilarsa ta dauki makami ta yaki wasu al’ummu na daban, babu shakka akwai matsala gagaruma. A wannan makon, GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci ne game da kalaman da tsohon Ministan Tsaro, Laftana Janar Theophilus Yakubu danjuma (mai ritaya) ya furta a ranar Asabar da ta gabata:

A ranar Asabar, 24-03-2018 ce aka gudanar da taron yaye dalibai na Jami’ar Jihar Taraba, a garin Jalingo. A ranar ce Laftana Janar T.Y. danjuma (mai ritaya) ya gabatar da wani jawabi, wanda ya tada hankalin al’ummar Najeriya kwata, jawabin da ya cika kafafen watsa labarai na gida da na waje.

Munin jawabin ya haddasa gawurtar labarin da kuma abin da yaka iya haifarwa na cutarwa ga al’umma. Kamar yadda al’amarin ya faru, tsohon sojan, wanda wadansu ke ganin cewa wutar kabilanci ce ta cinye zuciyarsa, ya bayyana cewa wai Sojin Najeriya sun gaza shawo kan rikice-rikicen da ke faruwa a kasar nan. Ya ce fadace-fadacen da ake alakantawa da Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa a sassan kasar nan, ya yi zargin wai hadin baki ne a tsakanin sojoji da Fulanin. A cewarsa, wai sojojin suna goyon bayan Fulani makiyaya, suna ba su kariya wajen fada da manoma.

Ga kadan daga abin da danjuma ya fada: “Sojoji na nuna son kai. Suna hada kai da mahara da ke dauke da bindiga suna kashe mutane, suna kashe ’yan Najeriya. Su ke ba su kariya a duk inda suka tafi. Idan kuka ce za ku dogara da sojoji don su hana kashe-kashen, za ku mutu daya bayan daya.

“Dole ne a kawo karshen yunkurin kawar da wata kabila a Jihar Taraba. Dole ne a tsai da kashe-kashen a dukan jihohin Najeriya, idan ba haka ba kuwa, abin da ya faru a kasar Somaliya zai zama kamar wasan yara. Ina kiran kowa da kowa da ya zauna cikin shiri kuma ku kare kasarku, ku kare yankinku, ku kare jiharku. Ba ku da wani wurin zuwa da ya wuce garinku.”

Abin da ya kara ta da hankalin jama’a dangane da wannan maganganu na tsohon sojan shi ne, yadda a lokuta daban-daban aka samu yi wa al’ummar Fulani makiyaya kisan gilla a yankin Mambila a Jihar Taraba. An kashe mata da maza, yara da manya, kamar kuma yadda aka kashe dabbobi da cinna wa dukiyoyinsu wuta.

Hankali ya tashi dangane da wadannan kalamai na danjuma saboda ganin yadda rikici ya ki ci ya ki cinyewa musamman a jihohin Benuwai da Nasarawa da Filato da sauransu. Hankali ya tashi ganin yadda mafi yawan wadanda ake kamawa da bindigogi da dama daga cikinsu ma ba Fulani makiyaya ba ne.

Mutane suna la’akari da cewa a halin da ake ciki, T. Y. danjuma fa ba karamin yaro ba ne, bana shekararsa 80 a duniya. Ya yi aikin soja, inda ya rike mukamai daban-daban a kasar nan, ciki har da Ministan Tsaro. Baya ga haka, shi hamshakin attajiri ne kuma shugaban al’umma wanda duk wani motsinsa kan iya yin tasiri ga al’umma.

Sanadiyyar wannan kalami, wanda ke kama da tunzura al’umma su dauki doka a hannunsu, wadansu mutane da dama sun yi ta nazari da tariyar tarihi, na yadda al’amura suka gudana a can baya. Wadansu na ganin cewa shin a lokacin da danjuma ke cikin kaki, wane irin aiki ya gudanar?

An waiga baya zuwa 1977, zamanin mulkin soja, karkashin shugabancin Obasanjo, lokacin da danjuma ke rike da mukamin Hafsan Askarawan Najeriya. A lokacin, an samu tabbacin cewa shi ne ya uzzura wa iyalan Kuti, inda ya sanya aka rushe Kalakuta Republic, gidan Fela. A sanadiyyar wannan rusau din, mahaifiyar Fela, Funmilayo Ransome Kuti ta rasu. Daga 1999 zuwa 2003, danjuma ne Ministan Tsaro a karkashin Gwamnatin Obasanjo. Bisa umarninsa sojoji suka ziyarci garuruwan Zaki-Biyam da Odi, inda suka karkashe al’umma masu yawa. Haka kuma an yi ta samun rikice-rikice tsakanin kabilarsa ta Jukun da kabilar Tibi, amma duk da haka bai fito ya yi yekuwar cewa al’umma su dauki makami su kashe juna ba sai yanzu.

Zuwa yanzu dai hukumomin tsaro da kungiyoyin al’umma suna ta Allah wadai da wannan kalami na danjuma. Hukumomin Sojan Najeriya sun barranta kansu da ikirarin da ya yi cewa suna goya wa wani bangare baya a yayin gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaro. Sun nuna yadda al’ummar Takum a Jihar Taraba suke kawo wa Soja cikas wajen gudanar da ayyukansu na samar da tsaro a yankin. Sun ba da misali da yadda a ranar 16 ga watan Maris din nan, mutanen Takum (kabilar danjuma) suka datse kan wani jami’in soja mai kwazo.

Bisa ga wannan kira da danjuma ya yi wa al’ummarsa, cewa su dauki makami su kare kansu, Sojan Najeriya sun yi gargadi, cewa duk wanda aka kama da makami, zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Haka ita ma kungiyar Kare Al’ummar Arewa ta Tsakiya (Middle Belt Conscience Guard) a nata bangaren, kokawa ta yi dangane da kalaman na tsohon soja, danjuma. Ta ce ya kamata a tuhume shi ya yi karin bayani karara na ainihin abin da yake nufi da kalaman nasa, domin kuwa a cewar kungiyar, kalamai ne da za su iya tayar da zaune-tsaye. Haka sun nemi hukumomin tsaro a Najeriya cewa, su dora wa T. Y. danjuma duk wani alhaki, idan har aka samu tashin hankali a Jihar Taraba sakamakon wannan ikirari nasa.

Magana ta gaskiya, ya kamata T. Y. danjuuma ya fito ya janye wadannan kalamai da ya yi a gaban jama’arsa, sannan ya ba al’umma hakuri. Haka ya kamata ba shi kadai ba ma, duk wani shugaban al’umma ko malamin addini ya rika kula da kalaman da zai furta a cikin al’umma, domin kuwa duk abin da suka furta, yana iya yin tasiri ga mabiyansu.

Babu abin da ake bukata a Najeriya illa zaman lafiya, zaman lafiya kuma ba zai taba samuwa ba sai an samu hadin kai da zaman tare da kishin kasa daga al’ummar kasa. Sai an cire wariya ta kabilanci ko addini ko bangaranci daga al’amuran yau da kullum. Lallai Najeriya tana fuskantar kalubalen tsaro, wanda ya zama wajibi a samu hanyoyi da matakan saita al’amura.