T.Y. danjuma ga Jonathan: Ka hanzarta kama Dokubo da Tompolo

Tsohon Ministan Tsaro Janar Theophilus Yakubu danjuma ya bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya hanzarta kama Alhaji Asari Dakubo da dukkan wadanda suka yi barazanar tayar da zaune-tsaye a kasar nan. Janar T. Y. danjuma ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Jami’ar Arewa maso Yamma […]

T.Y. danjuma ga Jonathan: Ka hanzarta kama Dokubo da Tompolo
T.Y. danjuma ga Jonathan: Ka hanzarta kama Dokubo da Tompolo

Tsohon Ministan Tsaro Janar Theophilus Yakubu danjuma ya bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya hanzarta kama Alhaji Asari Dakubo da dukkan wadanda suka yi barazanar tayar da zaune-tsaye a kasar nan.

Janar T. Y. danjuma ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Jami’ar Arewa maso Yamma da ke Kano jim kadan da kaddamar da Birnin Kwankwasiyya da gwamnatin Jihar Kano ta gina. Ya ce wajibi ne a hukunta tsofaffin ’yan ta’addan kan miyagun kalamansu.
A kwanakin baya ne tsofaffin ’yan ta’addan da suka hada da Mujahid Asari-Dokubo, shugaban kungiyar mayakan sa-kai ta Niger Delta Peoples bolunteer Force da bictor Ben Ebikabowei, da ake kira da Boy Loaf da Gobernment Ekpudomenowei da ake kira da Tompolo suka yi taro a Bayelsa, inda suka yi barazanar hargitsa kasar nan idan aka kayar da Shugaba Jonathan a zabe mai zuwa.
Janar danjuma ya bayyana kalaman nasu da muguwar tunzurawa da rura wutar gaba, kuma ya ce hadin kan kasar nan ba abu ne da za a yi wasa da shi ba.
“Kalaman rashin hankali ne da suka fito daga mutane marasa mutunci, kuma wajibi ne a la’ance su, kai ma ya wajaba a kama su,” inji Janar danjuma.
Ya bukaci ’yan siyasa su guji furta kalaman da za su harzuka jama’a, inda ya ce ’yan siyasa suna rike da makullan hade kan kasar nan wuri daya. “Ya kamata ’yan siyasa su guji yin kalaman da za su harzuka jama’a a lokacin da suke kamfe a wannan lokaci mai muhimmanci na babban zabe. Kamata ya yi a mayar da hankali kan batutwan da suka shafi kasa a lokacin kamfe,” inji shi.
Ya ce, “Ba mu da dabi’ar ci gaba hatta a cikin gwamnati daya, idan aka samu sauyin ministoci wadanda suka biyo baya galibi sukan yi watsi da abin da suka gada ne. Na baya kan yi watsi da abin da suka gada, fatata duk wanda zai gaje ka (Kwankwaso) ya ci gaba da kyakkyawan aikin da ka faro.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yanke shawarar gina biranen Kwankwasiyya da Amana da Bandirawo ne saboda ya rage cinkoson da birnin Kano ke fama da shi tare da magance matsalar karancin gidaje da rage matsin da ake fuskanta a gine-ginen gwamnati.
Ya ce, aikin gina wadannan birane uku a karkashin aikin ‘Babban Birnin Kano’ ya lashe kimanin Naira biliyan 30, inda ya ce tuni gwamnati ta sayar da kimanin gidaje 250 da fili mai girman hekta 41 ga wani kamfanin kasar China kan Naira biliyan biyar. Gwamnan ya ce za a sayar da sukkan gidajen da ke biranen uku nan da watan Mayun bana.