Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu

Wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa har lahira a lokacin da suka yi ƙazamin faɗa da ya ɓarke a gidansu sanadin taƙaddama

Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu

Wuka

Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sanar da kama Mista Peter Dike da ake zargi da kashe matarsa ​​a gidansu da ke Unguwar Oke-Ira Ilogbo Eremi, Marogbo.

Rundunar ’yan sandan a ranar Alhamis ta bayyana cewa wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa har lahira a lokacin da suka yi ƙazamin faɗa da ya ɓarke a gidan nasu sanadin taƙaddama a ranar Laraba.

Wannan mummunan al’amari ya ƙara dagula al’amuran tashin hankali a cikin gidan ma’aratan da ya kawo sanadin mutuwar matar aure.

A watan Oktoban 2024, an kuma kama Motunrayo Olaniyi da laifin daɓa wa amaryarsa, Olajumoke wuƙa har lahira, a yayin wata hatsaniya mai zafi a gidan su a rukunin gidaje na Amazing Grace Estate, Elepe, a yankin Ikorodu.

Da yake ƙarin haske kan lamarin a ranar Laraba, jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an sanar da jami’an tsaro na sashen Morogbo, kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka isa wurin.

Hundeyin ya ci gaba da cewa, “An tabbatar da al’amarin, bayan da jami’an ‘yan sanda da ke sintiri a cikin garin da ke yankin suka samu labarin, sai suka shiga cikin gaggawa suka cafke wanda ake zargin, an samu wuƙar kicin guda ɗaya da tabo da jini daga wajensa, aka kawo shi ofishin aka yi masa tambayoyi.

“Ya amsa laifinsa, an ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry, kuma za a miƙa ƙarar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, Panti Yaba.”