Taƙaddamar ɗaukar ’yan sanda 10,000 aiki
Daukar ’yan sanda 10,000 duk shekara zai rage karuwar mutanen da ka iya zama barazana ga kasa.
Ga duk wanda ya kwana ya tashi a Nijeriya ya san kasar nan tana fama da matsalar tsaro.
Kuma wannan ne ya sa tun a shekarar 2016 tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a dauki ’yan sanda 10,00 a aikin dan sanda, a watan Agustan 2015.
Kuma a watan Maris din 2016 lokacin da ya halarci wani babban taro kan tsaro a Abuja ya nanata hakan inda aka ce ana kan kokarin bin wannan umarni na Shugaban Kasa.
Daga baya tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a rika daukar kuratan ’yan sanda 10,000 duk shekara har na tsawon shekara shida, kamar yadda tsohon Ministan Harkokin ’Yan sanda Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi ya bayyana wa duniya.
- Tinubu da Atiku sun yaba da hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi
- Za a ci gaba da shari’a ba sai Ganduje ya halarci zaman kotu ba — Alƙali
A lokacin ma gwamnonin jihohi 36 na kasar nan har cewa suka yi daukar ’yan sanda 10,000 duk shekara ya kasa, saboda ana fama da karancin jami’an tsaro da za su yi aikin tabbatar da tsaro a kasar nan.
Har ma sun bayar da shawarar a dauki wadanda suka samu horo na tsawon shekara biyu a karkashin shirin NPower da kuma wadanda suka kammala horon yi wa kasa hidima ko wasu sanannun cibiyoyi a aikin dan sandan don karfafa Rundunar ’Yan sandan Nijeriya.
Sai dai babban abin takaici duk da munin matsalar tsaro a kasar nan sai ga shi bayan an dauki rukuni na farko sun gama samun horo saura a tura su wuraren aiki, sai aka shiga takaddama a tsakanin Hukumar Kula da Harkokin ’Yan sanda (PSC) da Rundunar ’Yan sanda ta Kasa (NPF) a kan wane ne yake da ikon daukar kuratan ’yan sanda 10,000 da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni.
Wannan takaddama ta bayyana ne a karshen watan Agustan shekarar 2019, inda a karshe Hukumar PSC ta dakatar da daukar kuratan ’yan sanda 10,000 har illa masha Allahu.
Kakakin Hukumar, Ikechukwu Ani, ya fadi a wata sanarwa a lokacin cewa tabbas an dakatar da aikin tantance sauran matakan da ake bi na daukar aikin.
Kuma hukumar tana gargadin dukkan masu neman aikin dan sanda su yi watsi da duk wani jerin sunayen da ke kunshe da bayanan wadanda suka samu nasarar samun aikin, domin ba daga gare ta yake ba.
Ani ya ce, aikin hukumarsu ce ta dauki ’yan Nijeriya a aikin dan sanda, ya’alla kurata ne ko sufetoci ko sufirtanda, kuma hukumar ba za ta yi sakaci da wannan muhimman aiki da aka dora mata ba.
An ruwaito cewa a lokacin Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu ya je ofishin Hukumar PSC ya shaida wa shugabanninta cewa aikin rundunarsa ce daukar kuratan ’yan sandan, wadanda har sun kammala jarrabawar fara aikin makonni kadan baya.
Bayanai sun ce a doka Hukumar PSC ce take da ikon daukar ’yan sanda aiki da ladabtar da su da yi masu karin girma, amma a baya hukumar ta amince NPF ta rika gudanar da aikin daukar kuratan ’yan sandan.
Shugaban Hukumar PSC na lokacin Alhaji Muslihu Smith ya amince da bukatar Sufeto Janar din, to amma inda gizo ke sakar shi ne, ma’aikatan Hukumar PSC sun riga sun yanke shawarar zuwa yajin aiki muddin aka bar aikin daukar ’yan sandan a hannun NPF.
Wannan takaddama ita jawo asarar daukar ’yan sanda dubu 60 ashekara shida na gwamnatin Buhari, inda sai a watan Oktoban 2023 aka ce an sasanta a tsakanin PSC da NPF don ci gaba da daukar ’yan sanda 10,000 da tsohon Shugaban Kasar ya amince.
Wani abin ban takaici da ban haushi, hukumomin biyu da suka ce sun sasanta ba su yi haka ba, sai bayan da Koton Koli ta yanke hukunci a kan takaddamar da suke yi wannan ne kuma ya jawo aka shafe wadannan shekaru ba tare da an dauki wadannan ’yan sanda ba.
A watan afrilun 2023, tsohon Shugaban Hukumar PSC, Mista Solomon Arase ya shaida wa duniya cewa ba za a sake samun takaddama a tsakanin hukumar da rundunar ba, amma kwatsam a wajejen karshen watan Yunin da ya gabata, sai ga wata sabuwa ta bayyana.
Domin bayan ana murnar cewa batun ya zo karshe har an tsara daukar ’yan sandan a wannan karo, yara sun gama wahalce-wahalcen tantacewa, kwatsam a watan na Yuni, sai ga rahoto na cewa Rundunar ’Yan sandan Nijeriya tana zargin rashin bin ka’ida da yin almundahana wajen daukar ’yan sandan a aiki.
Kuma a ranar 4 ga Yuni Hukumar PSC ta saki jerin sunayen wadanda suka samu nasara shiga aikin.
Amma bayan kwana 11 sai NPF ta yi wannan zargi ta hannun Kakakinta na Kasa, Muyiwa Adejobi wanda ya ce “Sunaye da dama da aka ce na wadanda suka samu nasara ce ko bukatar shiga aikin ba su rubuta ba balle su halarci horo da tantancewar.”
Wannan ya sa kungiyar ma’aikatan Hukumar PSC ta yi kiran a sauke Sufeto Janar Kayode Egbetokun kan bayar da bayanan karya, kuma a ranar 25 ga Yuni, Kakakin Hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya ce za su saki jerin sunaye na karshe kuma ba za su sauya ba, yana mai cewa an bi ka’ida wajen daukar kamar yadda dokoki suka tanada.
Wannan daukar aiki fa a hedikwatoci da cibiyoyin ’yan sanda aka yi, kuma ’yan sanda ne suka jagoranci akasarin aikin bayar da horo da tantancewa da sauransu.
Shi ya sa Hukumar PSC ta kalubalanci NPF kan ta kawo shaidar yin almundahana ko rashin gaskiya da aka yi a lokacin daukar aikin.
A daidai wannan lokaci da hukumomin biyu suke takaddama suna nuna wa juna kwanji kan ikon daukar ’yan sandan, a gefe guda kuma matsalolin tsaro suna ci gaba da tabarbarewa ne a sassan kasar nan.
Ta kai kusan kullum sai an sace mutane ko an kashe su ko an raunata su a dalilin ayyukan ’yan ta’addan Boko Haram da masu garkuwa da mutane da masu fashi da makami da masu son a raba kasa da rikicerikicen kungiyoyin asiri.
Nijeriya mai mutane sama da miliyan 216, kwata-kwata ’yan sanda dubu 371 da 800 take da su wato kowane dan sanda daya yana kula da sama da mutum 580.
Shin don Allah ta yaya za a samu tsaro a irin wannan yanayi? Domin baya ga karancin ’yan sandan, dan albashin da ake biyan akasarinsu da sauran jami’an tsaro da ma’aikata a kasar nan, ba zai ishe su rike kansu na mako biyu ba.
Alhali a gefe ga dimbin miyagu dauke da makaman da suka fi na jami’an tsaron kuma suna samu kudin da jami’an tsaron ba sa samu!
Tilas ne shugabannin kasar nan su rika nuna damuwa da halin da jama’a suke ciki ba, kada tunaninsu ya fi karkata kan yadda za su samu kudin yin ‘aiki’ don burge mutane.
Su sani sai mutum yana natse zai ga amfanin titin da suka yi ko makarantar da suka gina.
Don haka su tashi tsaye su yaki wannan kirkirarren talauci da tsarin Jari-Hujja da suka rungumo ya jefa jama’arsu a ciki.
Ko ba komai ba, daukar ’yan sanda 10,000 duk shekara kara samar da aikin yi ne da rage karuwar mutanen da ka iya zama barazana ga kasa, baya ga kara inganta tsaro da hakan zai yi.
Mun yaba sanya baki da Ministan Harkokin ’Yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam ya yi kan lamarin, kuma muna fata wannan ya zama na karshe da za a sake ssamun irin wannan takaddama a tsakanin PSC da NPF.
Kuma ya kamata Kungiyar NLC da takwaranta ta TUC su rika sa ido a kan kungiyoyin ma’aikata wadanda saboda bukatunsu na kashin kai suke jawo wa kasar nan matsala, kamar yadda suka nuna a kan wannan batu na daukar ’yan sanda aiki.
Idan mutane suna ganin ta haka ne za su tara kazamar dukiya, su sani sai da lafiya da zaman lafiya ake cin gajiyar dukiyar da aka tara. Su sani talauci da kwanciyar hankali ya fi dukiya da tashin hankali.