Ta auri maza bakwai don samun haihuwa da kowanensu
Yanayin rayuwar wannan mata ya sa wadansu suna tsoronta.
Wata mata ’yar asalin kasar Rwanda ta jefa jama’a cikin mamaki bayan ta auri maza bakwai, wacce ta kasance a duk tsawon rayuwarta ba ta taba aske gashin kanta ba.
Matar dai mai ba da maganin gargajiya ce, kuma ta auri maza bakwai da shirin kara auran wadansu a nan gaba.
- A Morocco za a yi wasan karshe na kofin zakarun nahiyyar Afirka
- An yi wa Ganduje rigakafin Coronavirus zagaye na biyu
Ta ce, duk mazan da ta aura tana ganinsu a matsayin dattawan rauhanai ne kafin ta aure su.
Ta aure su ne, saboda bukatar dattawan rauhananta, wadanda suka ce mata ta haifi yara da yawa sannan kowane mijinta zai haifi da guda ne kawai da ita, hakan ya sa a yanzu take da ’ya’ya shida da mazan.
Matar ta ce tana taimaka wa marasa lafiya ne da karfin matattu.
A cewarta, ta yi imani mutanen kirki da suka mutu ba za su bari jama’arsu su wahala ba, don haka suka ba ta lakanin warkarwa.
Ta ki yarda da ta aske gashin kanta ne, saboda hakan kamar wani garkuwa ne gare ta.
Duk da auren maza bakwai da ta yi, tana daukar dawainiyarsu tare da gina wa kowane miji gida, takan zabi lokacin da kowane mijin zai kasance tare da ita, sannan ba namijin da zai yi kuskuren cutar da ita, kuma suna fita shakatawa tare da ita.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, yanayin rayuwar wannan mata ya sa wadansu suna tsoronta.