Ta babbaka mijinta da ruwan zafi kan robar wanka

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen karamar Hukumar Dala, ta cafke wata matar aure mai kimanin shekaru 20 mai suna Maimuna Usman saboda babbake mijinta da tafasasshen ruwa a dalilin wani sabani da ya shiga tsakaninsu.Rahotanni sun  bayyana cewa ba mijin nata kadai ta babbake ba, har da wani makwabcinsu da ya shiga gidan don […]

Ta babbaka mijinta da ruwan zafi kan robar wanka
Ta babbaka mijinta da ruwan zafi kan robar wanka

Malam Muhammad Sani yana jinya bayan matarsa ta sheka masa ruwan zafiHukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen karamar Hukumar Dala, ta cafke wata matar aure mai kimanin shekaru 20 mai suna Maimuna Usman saboda babbake mijinta da tafasasshen ruwa a dalilin wani sabani da ya shiga tsakaninsu.
Rahotanni sun  bayyana cewa ba mijin nata kadai ta babbake ba, har da wani makwabcinsu da ya shiga gidan don yin sulhu.
Malam Muhamamd Sani, wanda aka fi sani da Mai kaho, mazaunin unguwar Kurna Gobirawa ne cikin yankin karamar Hukumar Dala, wanda kuma mai kimanin shekaru 58 ne, ya shaida wa Aminiya cewa matar tasa ta sheka masa ruwan zafin ne a kan ya nemi roba zai yi wanka, ita kuma matar ta hana shi, lamarin da ya sa shi kuma ya kai mata duka, daga nan ta dauki tukunyar ruwan zafi da ke tafasa a kan wuta ta sheka masa.
“Lokacin da na nemi ta ba ni robar wanka, sai ta ce wai ba za ta ba ni ba, domin ita ta sayi abarta. Ba yadda ban yi da ita ta ba ni robar  na yi wanka ba, amma ta ki. Hakan ya fusata ni har na kai mata duka, sai ga wani makwabcina ya shigo ya rike ni, yana ba ni hakuri. Ba mu sani ba, ashe ta dauko ruwan zafin da za ta dama koko da shi, sai ji muka yi ta kwara mana a jikinmu. Hakan ya jawo dukkanin kaina da fuskata da wuyana ya babbake, shi kuma makwabcina ya kone a hannuwansa”.
Malam Mai kaho, wanda tsohon mafarauci ne, ya kara da cewa, “Da ma mun dade muna samun matsala a tsakaninmu, domin sau biyu muna zuwa Hukumar Hisba ana yi mana sulhu, sai dai a wannan karon ne ta dauki wannan matakin na ganin ta sabauta ni. Ni duk abin da ke ba ni mamaki da wannan lamarin gaba daya shi ne tsawon lokacin da na dauka ina farauta, babu bindiga ko wuka da suka taba huda jikina, amma sai ga shi yau mace na neman zama ajalina”.
A nata bangaren Maimuna, wacce ke gab da haihuwa, ta yi wa Aminiya bayanin cewa, lallai ya nemi ta ba shi robar wanka, “Da ma akwai laifin da ya yi min, don haka na hana shi. Shi ke nan sai na ji ya shake ni, yana dukana. Jin zafin dukan da yake min da kuma ganin ina dauke da juna biyu, amma bai duba hakan ba, ya sa ni ma na dauki matakin kare kaina”. Inji ta.
Amarya Maimuna, wacce ke cikin yanayin da-na-sani, ta nemi afuwar mijin nata tare da hukuma kan su yafe mata laifin da ta aikata. “Wallahi, ban san abin zai zama haka ba. Amma ina neman a yi min afuwa. Kuma ni ina son mijina, don ba zaman kiyayya muke yi ba”. Inji ta.
Shi kuma a nasa bangaren, makwabcinsu Malam Abdul’azeez Mai Faskare, ya bayyana yadda ya sami rabonsa cikin wannan waki’a. Ya ce, “Rabon fada na zo yi ganin cewa karfin mace da namiji ba daya ba ne, ga shi kuma tana dauke da juna biyu, hakan ya sa na shiga tsakaninsu, na rike masa hannu. Ban san abin da ke faruwa ba, sai na ji yana cewa ‘ta kona ni’. Ina dubawa, sai na ga ashe ni ma na samu nawa rabon, domin hannuwana duk sun kone”.
 Maimuna, wadda ta sheka wa mijinta ruwan zafiDangane da matsayin cigaba da dorewar zaman auren nasu, Malam Mai kaho ya ce atabau, ba zai ci gaba da zama da ita a matsayin matarsa ba, saboda bai san gaba me za ta aikata masa ba. “A gaskiya ba zan ci gaba da zama da ita ba, domin da ma ta dade tana son ta aikata min wani mummunan abu, sai yanzu ne ta samu dama. Duk mutumin da ya kona ka, to Allah ne kadai Ya san abin da zai aikata maka nan gaba. Ni dai na yafe wannan aure”. Inji shi.
Abubakar Mati Salihu shi ne Mataimakin Shugaban Hukumar Hisba a karamar Hukumar Dala ya bayyana wa Aminiya cewa hukuma ba za ta kyale wannan mai laifi ba. “Kasancewar mun sha yin sulhu a tsakanin wadannan ma’aurata, amma abubuwa sun ki daidaituwa, don haka ba za mu kyale wannan lamari haka ba. Za mu gurfanar da ita a gaban kuliya domin ta girbi abin da ta shuka, sannan kuma don ya zama darasi ga masu hali irin nata”. Inji shi.