Ta banka wa kanta wuta saboda ta kama saurayinta da wata

Wata budurwa mai suna Bilkisu ’yar asalin Jihar Kano ta banka wa kanta wuta bayan da ta kama saurayinta da wata budurwa. Wannan abu ya auku ne a Layin Sarkin Fawa da ke garin Samaru, a ranar Larabar makon jiya.Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun shaida wa Aminiya cewa budurwar ta baro gidansu […]

Ta banka wa kanta wuta saboda ta kama saurayinta da wata
Ta banka wa kanta wuta saboda ta kama saurayinta da wata

Wata budurwa mai suna Bilkisu ’yar asalin Jihar Kano ta banka wa kanta wuta bayan da ta kama saurayinta da wata budurwa.
Wannan abu ya auku ne a Layin Sarkin Fawa da ke garin Samaru, a ranar Larabar makon jiya.
Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun shaida wa Aminiya cewa budurwar ta baro gidansu ne a cikin birnin Kano kimanin shekara uku da suka wuce inda ta dawo Zariya tana zaman kanta.
“Wannan yarinya ina ganin za ta kai kimanin shekara ashirin,” inji wani da abin ya faru a kan idonsa mai suna Abdul’azeez Anlalo. Ya ce “A Zariya ta shiga sana’ar rawa ne da ake kira rawar Mami ko rawar Solo, inda a wasu lokuta mace za ta iya yin tsirara. Daga nan wanda ya yi sha’awarta sai ya zo ya fanshe ta. In ba a samu mai fansarta ba, sai shugabannin rawar su rika zuba mata ruwan bula ko na kwata a cikin al’aura.”
Anlalo ya ce ranar da abin ya faru wasu mutane ne suka zo a guje suka shaida masa cewa ga Bilkisu can ta sa wa kanta wuta. “Ina zuwa gidan da take sai na ganta tana cin wuta. Muka yi kokarin kashe wutar amma ta riga ta yi mata illa.Bayan kashe wutar ne na nemo mota muka garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika. Daga nan muka fara neman inda za a samu ’yan uwanta. Da muka matsa da bincike sai kawarta da suka fito yawo tare ta ba mu adireshin inda za mu samu gidansu,” inji Anlalo.
Ya ce bayan da aka samu gidan su Bilkisu ne mahaifiyarta ta zo Zariya, sai dai zuwanta da kwana daya Bilkisu ta ce ga garinku nan.
Wakilinmu ya ga mahaifiyar Bilkisu a gigice bayan da ta ga an turo gawarta ta a cikin kura ana kokarin sanya ta a mota don tafiya da ita garinsu.
Duk kokarin da ya yi don jin ta bakin mahaifiyar Bilkisu ya ci tura saboda ko magana ba ta yi da kowa.
Shi kuwa saurayin Bilkisu mai suna Miyatti, daga jin labarin abin da ya faru sai ya cika wa rigarsa iska don gudun shiga hannun ’yan sanda, kamar yadda wasu jama’ar Samaru suka shaida wa Aminiya.
Wani jami’in ’yan sanda a hedkwatar shiyya da ke Zariya ya shaida wa Aminiya cewa ’yan sanda sun fara bincike kan lamarin, inda suka kama mai gidan rawar da su Bilkisu ke cashewa.
“Mai gidan rawar sunansa Yakubu, mun gayyato shi ya gaya mana abin da ya sani kuma muna ci gaba da bincike, amma zuwa yanzu abin da muka gano shi ne ita yarinyar da kanta ta kona kanta saboda kishi,” inji jami’in wanda ba ya so a ambaci sunansa.