Ta bayyana maganin yi wa matan aure fyade
Wata mai rajin kare ’yancin mata a Jihar Gombe, Hajiya Fati Usman Kulani ta nuna bakin ciki kan yadda wasu da ta kira marasa albarka suke sace matan aure suna yi musu fyaxe sannan su kashe su.Hajiya Fati Kulani, wadda fitacciyar ’yar jarida ce a Gombe ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa […]
Wata mai rajin kare ’yancin mata a Jihar Gombe, Hajiya Fati Usman Kulani ta nuna bakin ciki kan yadda wasu da ta kira marasa albarka suke sace matan aure suna yi musu fyaxe sannan su kashe su.
Hajiya Fati Kulani, wadda fitacciyar ’yar jarida ce a Gombe ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Gombe inda ta ce babu abin da za a yi kan wannan bala’i na sace matan aure ana yi musu fyaxe kuma a kashe su.
Fati Kulani ta yi kira ga matan aure da zawara da waxanda ba su da aure su yi rika taka-tsantsan domin waxansu matan na fuskantar fyaxe ne saboda irin yadda suke sanya tufafi kamar za su yi tafiya kusan tsirara.
Ta bukaci teloli da suke yi wa mata banzan xinki da ke xame su yana fitar da surar jikinsu su ji tsoron Allah su daina, domin suna taimakawa wajen lalacewar mata.
Fati Kulani ta yi kira ga magidanta su yi kokari su fi karfin matansu wajen hana su fita ba bisa ka’ida ba, domin kauce wa aukawa cikin tarkon batagari idan kuma fitar ta zama dole to a haxa su da ’yan rakiya.
Sai ta bukaci Majalisar Tarayya ta bullo da wata doka da za ta sa duk wanda aka kama da laifin fyaxe ga mata manya ko kanana a yi masa xaurin rai-da-rai don ya zama darasi ga sauran.