Ta biya kudin wayar iPhone6 Naira 36,000 an ba ta kwalin dankali

Wata mata a Amurka ta biya kudin sayen wayar alfarma ta iPhone6 kan Dala 100 a ranar rahusar kayayyaki ta ‘Black Friday,’ amma cikin rashin sa’a tana bude kwalin wayar sai ta samu ferarren dalin guntu-guntu har guda 11. Matar ta baza hoton bidiyon wannan al’amari da ya faru a shafin sadarwa na Libeleak, inda […]

Ta biya kudin wayar iPhone6 Naira 36,000 an ba ta kwalin dankali

Wata mata a Amurka ta biya kudin sayen wayar alfarma ta iPhone6 kan Dala 100 a ranar rahusar kayayyaki ta ‘Black Friday,’ amma cikin rashin sa’a tana bude kwalin wayar sai ta samu ferarren dalin guntu-guntu har guda 11.

Matar ta baza hoton bidiyon wannan al’amari da ya faru a shafin sadarwa na Libeleak, inda aka ga kwalin wayar alfarma ta iPhone6 cike da dankali ferarre.

Matar ta ce ta sayi wayar ne a wata katuwar mota cike da kaya da ke yawo a Wisconsin, dauke da hotunan kayayyaki da ake sayarwa cikin saukin farashi a ranar rahusa ta Black Friday. Ta ce motar na dauke da sauran kayayyakin da suka ahda da suture da takalma da agoguna da faya-fayan DbD da CD da wayoyin hannu da kwamfutar tafi-da-gidanka ta Laptops.

“Mutumin da ke tsayar da kayayyaki a motar har ragi ya yi mini, inda ya sayar mini kan Dala 100 (wato Naira 36,000). Ina ta wasa da kwalin wayar ina jujjuyawa. sai na tambaye shi ya kira sunan wayar, sai ya ba ni lamba, na ce ina sonta,” a cewar matar da ba a ambaci sunanta ba.

Sai dai lokacin da ta isa gida, sai ta gano cewa mutumin ya damfare ne, inda ya sayar mata da dankali maimakon waya. “Ina zaune a dakin girki sai na bude kwalin da aka sayar mini. Ga shi kwalin na dan nauyi, amma da budawa sai na naga dankali,” inji ta.

Kwalin (dankalin) dai yana dauke wayar caji.