Ta bukaci a raba aurenta saboda  mijinta bai son wanka

Wata matar aure mai suna Soni Debi, mai shekara 20 da ke zaune a Lardin Bihar’s Baishali a kasar Indiya, ta kai karar mijinta kotu tana neman a raba aurensu, saboda sau daya yake wanka a bayan kwana 10. Soni Debi, ta shigar da karar mijinta ne saboda rashin tsabtarsa sannan ta ce ba ya […]

Ta bukaci a raba aurenta saboda  mijinta bai son wanka

Wata matar aure mai suna Soni Debi, mai shekara 20 da ke zaune a Lardin Bihar’s Baishali a kasar Indiya, ta kai karar mijinta kotu tana neman a raba aurensu, saboda sau daya yake wanka a bayan kwana 10.

Soni Debi, ta shigar da karar mijinta ne saboda rashin tsabtarsa sannan ta ce ba ya da dabi’u masu kyau. Ta yi nadamar auren mijin mai shekara 23, mai sana’ar gyaran fanfo wadda ta ce ya dade yana cutar da rayuwarta. A cikin takardar karar da ta shigar Soni, ta ce abu ne mai wahala a same shi yana wanka ko yana wanke hakoransa kuma ba ya da abin da zamantakewar aure ta tanada, don haka ta bukaci kotun ta raba aurensu.

“Mijina yana wari saboda rashin yin aski da wanka kuma ba ya wanka sai bayan kwana 10. Sannan ba ya wanke bakinsa, ba ya da dabi’a mai kyau,” Soni ta rubuta. “A yanzu haka ba na bukatar ta ci gaba da kasancewa tare da mijina nan gaba. Ina bukatar a raba aurenmu da wanda ke kuntata wa rayuwata,” inji ta.

Ta ce: “Ba mu samu haihuwa da mijina ba, kuma dangantakarmu ba tsabtatacciya ba ce a matsayin ma’aurata. Irin wannan rayuwar ba ta da wata manufa,” kamar yadda matar ta tabbatar, inda ta ce tana bukatar mijin nata ya maida mata zinare na da wasu abubuwa masu daraja da iyayenta suka ba ta lokacin aurensu.

Mambobin Hukumar Mata ta Jihar (SWC) sun bai wa ma’auratan wa’adin wata biyu su sasanta kansu kafin su fuskanci kotu don raba auren nasu.

Mijin Soni mai suna Manish Ram, ya bayyana wa jaridar Times ta Indiya cewa, bai amince a raba aurensu da matarsa ba yana bukatar ci gaba da zama da ita kuma nan gaba zai gyara kura-kurensa.