Ta bukaci gwamnati da majalisa su kawo karshen takladdamar da suke yi kan kasafi

kungiyar Masu Kishin kasa da Shugabanci Nagari (CCGGT) reshen Jihar Filato ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta kasa su kawo karshen sa-toka-sa-katsin da suke yi kan kasafin kudin bana.Shugaban kungiyar, Malam Ahmed Hamza ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a ranar Litinin da ta gabata, inda […]

Ta bukaci gwamnati da majalisa su kawo karshen takladdamar da suke yi kan kasafi
Ta bukaci gwamnati da majalisa su kawo karshen takladdamar da suke yi kan kasafi

kungiyar Masu Kishin kasa da Shugabanci Nagari (CCGGT) reshen Jihar Filato ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta kasa su kawo karshen sa-toka-sa-katsin da suke yi kan kasafin kudin bana.
Shugaban kungiyar, Malam Ahmed Hamza ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a ranar Litinin da ta gabata, inda ya tunatar da bangarorin biyu halin da talakawan kasar nan suke ciki sakamakon takaddamar da ke wakana tsakaninsu. Ya ce kungiyar ta damu da yadda rikicin ya jefa talakawa cikin mawuyacin hali, kuma idan al’amura ba su daidaita ba halin kuncin da za su sake shiga ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba.
Ahmed Hamza ya bukaci bangarorin su hada kansu su yi aiki tare cikin kwanciyar hankali don hakan ya ba Gwamnatin Tarayya damar yin ayyukan ci gaban da za su amfani talakawa.
 “Takaddamar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa ba abu ne dai zai haifar wa kasar nan da mai ido ba, hakan ya kawo tsaiko ga kasafin kudin bana, ya kuma sanyaya gwiwar talakawa game da fatar da suke da ita ta samun kyakkyawar rayuwa a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari. Don haka muna son bangarorin biyu su fahimci cewa komai ya tsaya cik, talakawa suna cikin mawuyancin hali, ya kamata su sasanta su hada kansu don kawo karshen takaddamr da ke tsakaninsu, yin hakan zai ba Gwamnatin Tarayya damar yi wa talakawa ayyukan inganta rayuwa,” inji shi.
Ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta mika kokon bararta ga duk inda take ganin za a taimaka mata don ta shawo kan matsalar da ta hana tattalin arzikin kasar nan rawar gaban hantsi.