Ta bukaci kotu ta raba aurenta

Wata matar aure mai suna Sakina Saleh da ke garin Gwagwa, Abuja, ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta da suke zaman aure sama da shekara 8, kan zargin cewa ya bar gida na tsawon shekara daya da wata uku a yanzu. Sakina, wadda ta shigar da karar a Babban Kotun Lardi da ke […]

Ta bukaci kotu ta raba aurenta

Wata matar aure mai suna Sakina Saleh da ke garin Gwagwa, Abuja, ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta da suke zaman aure sama da shekara 8, kan zargin cewa ya bar gida na tsawon shekara daya da wata uku a yanzu.

Sakina, wadda ta shigar da karar a Babban Kotun Lardi da ke garin Gwagwa,Abuja, ta yi korafin cewa mijin nata mai suna Basiru Auwal, wanda ya bar gidansu da nufin zuwa ci-rani a garin Yola na Jihar Adamawa, ba a samunsa a lambarsa ta waya tun bayan tafiyar tasa, sannan babu labarinsa. Ta ce bayan karewar abincin da ya bar mata mako guda bayan tafiyar, wani dan uwanta ya taimaka mata da jarin fara sana’a a gida don kulawa da kanta da kuma dansu mai shekara daya. Sai dai a cewarta, tuni ta koma wajen iyayenta bayan da jarin da take sana’ar da shi, bukatu suka cinye shi.

Alkalin Kotun, Adam H. Aliyu ya ba da umarnin a aika wani zuwa inda ake tsammanin mijin nata yake da nufin cigiyarsa. Ya ce kotun za ta sake zama nan gaba a kan lamarin bayan kwana 40 daga lokacin da aka yi tafiyar.