Ta bukaci maza su rika ba mata damar tsayawa takarar siyasa

Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC ta karamar Hukumar Hawul a Jihar Borno Malama Hassana Ali Garba, ta ce burin mata na hawa mukaman da suka jima suna nema a siyasa ba zai cika ba har sai maza suna barin matan suna fita ana damawa da su a fagen siyasa.Malama Hassana Ali Garba, ta bayyana […]

Ta bukaci maza su rika ba mata damar tsayawa takarar siyasa
Ta bukaci maza su rika ba mata damar tsayawa takarar siyasa

Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC ta karamar Hukumar Hawul a Jihar Borno Malama Hassana Ali Garba, ta ce burin mata na hawa mukaman da suka jima suna nema a siyasa ba zai cika ba har sai maza suna barin matan suna fita ana damawa da su a fagen siyasa.
Malama Hassana Ali Garba, ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da Aminiya a ziyarar aiki da ta kai Gombe, inda ta nuna rashin jin dadi kan yadda aka bar mata a baya ta hana su fitowa takarar siyasa ko ba su mukamai na akalla kashi 35.
Ta yaba wa Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kasim Shettima bisa yadda ya rungumi al’ummar jihar ba tare da nuna bambancin siyasa ko kabila ba, inda suke cin ribar mulkin siyasa musamman yadda ya sanya mata a cikin gwamnatinsa.
Mataimakiyar Shugabar ta ce a karamar hukumarsu ta Hawul suna da matan da suka dace su fito takara tun daga kan kansila zuwa shugaban karamar hukuma da ’yan majalisar jiha da ta tarayya da sanatoci amma rashin ba su dama ya sa suna dari-darin fitowa saboda sun san maza ba za su ba su dama ba.
Malama Hassana Garba ta kuma bukaci gwamnati ta samar wa mata da wata hanya ta dogara da kai da za ta taimaka musu wajen tsayawa da kafafunsu kamar samar musu da kekunan dinki ko injunan yin taliya ko na saka da sauran sana’o’i.
Hassana Garba, ta yi amfani da jinjina wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin Najeriya kan yadda suke aiki ba dare ba rana wajen kawo karshen Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Ta ce a baya an rufe hanyar da ta tashi daga Biu zuwa Gombe saboda rikicin Boko Haram amma yanzu da al’amura suka fara daidai an bude hanyar ta nan ma suka shigo Gombe ba tare da sun ci karo da miyagu masu tada kayar baya a hanyar ba. Sai ta bukaci al’ummar Arewa maso Gabas su ci gaba da bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro hadin kai da goyon baya don su gudanar da aikinsu yadda ya dace.