Ta burma wa kishiyarta mai juna biyu wuka a ciki
Wata uwargida a Unguwar Gaida a karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano ta burma wa kishiyarta da ke dauke da juna biyu wuka a cikinta. Uwargidan mai suna Zulaiha Jibrin ta yi aika-aikar ne lokacin da kishiyarta ta zaga bandaki inda ta bi bayanta ta daba mata wukar.Bayanai sun ce babu wani sabani a tsakanin […]
Wata uwargida a Unguwar Gaida a karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano ta burma wa kishiyarta da ke dauke da juna biyu wuka a cikinta.
Uwargidan mai suna Zulaiha Jibrin ta yi aika-aikar ne lokacin da kishiyarta ta zaga bandaki inda ta bi bayanta ta daba mata wukar.
Bayanai sun ce babu wani sabani a tsakanin kishiyoyin biyu, inda aka ce a daren wayewar garin da lamarin ya auku tare suka je unguwa.
Amaryar mai suna Usaina Jibrin da take kwance a asibiti ta shaida wa Aminiya cewa, “Bayan mijinmu ya fita kasuwa sai na zaga bandaki. Ina kokarin fitowa ban san hawa ko sauka ba sai na ga abokiyar zamana ta yi kaina da wuka. Sai na tambaye ta laifin da na yi mata, sai ta ce tunda na auri mijinta sai ta kashe ni. Sai ta shiga daba min wukar. Na yi kokarin in kwace wukar amma na kasa, haka ta caccaka min wuka a ciki da hannu da baya da cinyata,” inji ta.
Game da ko akwai rashin jituwa a tsakaninsu, sai ta ce tunda ta aka kai ta gidan ba su taba fada ba, kuma kishiyar ba ta taba nuna mata wani hali marar kyau koda a fuskarta ba.
Amaryar ta ce duk da cewa cikinta bai zube ba sakamakon raunin da ta yi mata, sai dai tana fama da matsanancin ciwon ciki.
Mijinsu Malam Jibrin Yunusa, ya bayyana wa Aminiya cewa, “Babu abin da zan ce sai dai in ce Allah Ya shiryi uwargidana da ta aikata wanann danyen aiki, ita kuma amarya da ke a asibiti Allah Ya ba ta lafiya.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, uwargidan da ake zargin tana hannunsu kuma da zarar sun gudanar da bincike za su gurfanar da ita gaban kotu.