Ta cinna wa gidan mijinta wuta bisa zarginsa da neman mata
Wata mata mai suna Madam Rita da ke garin Dutse Baupma a yankin Bwari a Birnin Tarayya Abuja, ta banka wa gidansu wuta, inda daukacin dukiyar da ke cikinsa ta kone kurmus. Matar, uwar ’ya’ya hudu da uku suka gama karatu, a yayin da dan autansu ke wata jami’a, ta dauki matakin ne bisa zargin […]

Wata mata mai suna Madam Rita da ke garin Dutse Baupma a yankin Bwari a Birnin Tarayya Abuja, ta banka wa gidansu wuta, inda daukacin dukiyar da ke cikinsa ta kone kurmus.
Matar, uwar ’ya’ya hudu da uku suka gama karatu, a yayin da dan autansu ke wata jami’a, ta dauki matakin ne bisa zargin mijinta na lalata da wasu mata, kamar yadda wasu makwabtanta suka shaida wa wakilinmu.
Wani jagoran ’yan sintiri a Dutse mai suna Ijoba Darosa da ke makwabtaka da gidan, ya ce, yana kishingide a gida da misalin karfe biyar na asubahin ranar Asabar da ta gabata, sai matarsa ta shaida masa cewa, ta ji hayaniyar buge-buge a waje kuma tana zaton’yan fashi ne suka shigo, da ya fita sai yya ga ashe wuta ce, ana kokarin kalle gidan wanda matar ta rufe daga waje, don hana mijinta da ’ya’yansu biyu da wasu mutane fitowa daga ciki.
Ya ce, “A nan muka yi kokarin kashe wutar da wasu ’yan garuwa, muna cikin haka ne sai muka kula da wani daki da yaransu biyu ke ciki, suna ta buge-bugen neman kukuta bayan ya kama da wuta. Mun iske mijin a cikin gidan wanda ya shaida mana cewa dakinsa yana bude lokacin da matar ta fita da asubahi. Sai dai ya yi tunanin ta fita ne don sayo burodi kamar yadda ta saba, don sayarwa a shagonta da ke kofar gida.”
Jagoran ’yan bangan ya ce, bayan bude dakin da yaran ke ciki, sun yi ta nuna damuwa kan rashin ganin mahaifiyarsu suka shiga nemanta a dakunan gidan don kukutar da ita, amma daga bisani aka hango ta a waje ba tare da nuna damuwa kan al’amarin da ya faru ba.
Wata makwabciyarsu mai suna Fatima Muhammad, ta shaida wa Aminiya cewa, “Da farko na dauka janareta ne ya haddasa gobarar, amma bayan na jajanta mata ne, sai ta ce, ai ita ce ta cinna wutar da hannunta, don ladabtar da mijinta sakamakon neme-nemen mata da ta ce yake yi.”
’Ya’yanta biyu da suka yi ta nemanta don kukutar da ita da kyar da jikin goshi suka kwace ta daga hannun wani daya danta da ya rika dukanta bayan an gano ita ta banka wutar, saboda takaicin konewar takardun makarantunsa, inda ya rika cewa ta kata masa rayuwa.
Jami’an tsaro na Cikil Defense sun kama matar tare da mikata ga ofishin ’yan sanda na garin Dutse.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, DSP Hyelhira Altine Daniel ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ta shaida wa Aminiya cewa da zarar sun kammala bincike a kan al’amarin, za su gurfanar da matar a gaban kotu.