Ta daba wa karen saurayinta wuka saboda kishi

’Yan sanda sun kama wata mata a garin Niagara Falls a Jihar New York da ke Amurka, kan zarginta da daba wa karen saurayinta wuka saboda kishi. ’Yan sandan sun kama matar ce bayan saurayin ya kira wayarsu cewa, budurwarsa ta daba wa karensa wuka. Bayan zuwan ’yan sandan sun samu karen jini na zuba […]

Ta daba wa karen saurayinta wuka saboda kishi

Karen da aka dava wa wuqar

’Yan sanda sun kama wata mata a garin Niagara Falls a Jihar New York da ke Amurka, kan zarginta da daba wa karen saurayinta wuka saboda kishi.

’Yan sandan sun kama matar ce bayan saurayin ya kira wayarsu cewa, budurwarsa ta daba wa karensa wuka.

Bayan zuwan ’yan sandan sun samu karen jini na zuba a jikinsa sanadiyyar wukar da budurwar ta daba masa, inda tun daga baya har zuwa wuyansa jini ke zuba sannan ga wukar nan a gefe a gidan.

Sai dai ’yan sandan sun gano cewa, matar mai suna Christina Leighton mai shekara 54 ta sha giya ce lokacin da ta aikata hakan.

An kai karen mai suna Two Socks zuwa asibitin dabbobi na Niagara inda aka yi masa tiyatar gaggawa. Likitan dabbobin asibitin ya ce, karen ya samu raunin da ya kai tsawon inci uku a wuyansa kuma za a ci gaba da jinyar raunin a asibitin har zuwa lokacin da zai warke.

Rahoton da ’yan sanda suka fitar ya bayyana cewa, matar ta aikata hakan ne saboda saurayin nata da aka sakaya sunansa ya fi ba karen lokacinsa fiye da ita. Kuma kishin bai wa karenn irin wannan lokaci ne ya sa ta yanke wannan hukunci a kan karen.